Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jaridar Bunkasa Kasuwanci da Siyasa
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Wasanni

TARIHIN REAL MADRID

Daga Abdullahi Usman Tumburkai

Za mu fara ba da wannan tarihi ne daga shekarar 1992, saboda abin ba zai yiwu ba, mu ce za mu fara daga shekaru 100 din da kulob din ya yi yana raye.

Samun wani kulob din wasan kwallo da ya haura shekaru 100, da ke da kyakkyawan tarihi irin na Real Madrid, kusan a ce babu, musamman idan aka yi la'akari da irin ci gaban da kulob din ke samu ta kowace fuska. Sannan kuma a kusan kowace rana sunan wannan kulob din na zagaya duniya,don haka ne muke son sanar da ku wasu muhimman abubuwa dangane da kulob din yanzu.

A ranar 6 ga watan Maris na shekarar 1992, Real Madrid ta cika shekaru 90 da kafuwa. Kuma a wannan lokacin ne aka yi nazarin irin hawa da gangarar da kulob din ya yi har ya kai ga wannan matsayi. Wato abin da ya shafi bakin ciki da kuma farin ciki da kungiyar ta yi.

A 2 ga Afrilun 1992 ne duniyar wasa ta Real Madrid, ko mu ce 'yan Madrid sun rasa babban dan wasansu, Juan Gomez, "Juanito" wanda ya rasa ransa a hadarin mota lokacin da yake dawowa daga Merida, kallon wasan Real Madrid da Torino a filin wasa na Bernabeu.

A kuma ranar 26 Yuni ne na shekarar 1993, Real Madrid ta ci kofin kalubale na kasar a karo na goma sha bakwai bayan ta lallasa Zaragoza da ci 2 da 0. Wadanda suka ci wasan kuwa sune Emilio Butragueno da Mikel Lasa.

A 16 ga Disambar 1993, a kuma Nau camp, lokacin da aka dawo da wasan "Super Cup" Real Madrid ta yi kunnen doki da Barcelona. Kuma ita ka dau kofin sakamakon wasan da aka yi na farko a Madrid wato a filin wasa na Santiago Bernabeu, a ranar 2 ga watan Disambar shekarar, Real Madrid ta sami nasara kan Barcelona da ci 3 da 1.

Ran 7 ga watan Mayu 1994 aka yi wata karawa tsakanin Real Madrid da Barcelona a Bernabeu. Wannan karawar ba a taba samun 'yan kallo irinta ba a baya.

Real Madrid ta dau kofin "Iberia" bayan ta lallasa Boca Juniors da ci 4 da 3. Inda wasan farko aka yi a Bernabeu ran 27 ga Mayu 1994. Nan ne Madrid ta tashi da ci 3 da 1. Yayin da a karawa ta biyu a filin wasa na Buenos Aires, kungiyar Boca ta kasar Argentina ta sami nasara da ci 2 da 1.

Ran daya ga Yuli ne, Jorge Valdano ya zama Kochi a Real Madrid. Jorge ya zo da tabbacin cewa zai karbo kofin nan na "Champions League"da kuma sauran kofinan da ya cinye wa ita Real Madrid din lokacin da yake jagorantar kulob din Tenerife.

A zamanin wannan Koci, ya samo 'yan wasa kamar su Fernando Redondo, Laudrup, Amavisca, Quique Flores da kuma Canzares.

A 8 ga Junairun 1995 ne, aka yi wani wasa da ake masa lakabi da wasan karni. Real Madrid karkashin jagorancin Jorge ta lallasa Barcelona da ci 5 da 0. Dan wasa Zamorano ne ya ci kwallo 3 a wasan.

Duk dai a wannan shekarar, 19 ga watan Faburairu aka zabi Ramon Mendoza a matsayin shugaban kungiyar wasa ta Real Madrid, inda ya kada abokin hamayyarsa Florentino Perez da kuri'u 698. Inda kuma Gomez Pintado ya zama na uku.

Bayan shekaru biyar, Bernabeu ta sake rike kambinta na "Champion League". Wato dai a 1995 din. Wanda kuma shi ne karo na 26, da fara wasan Champion League. A nan ne Shugaban hukumar kwallon kasar ta Sifen Angel Maria, ya mika kofin ga Kaftin din Real Madrid, wato Manuel Sanchis. An kuma zabi Lorenzo Sanz ya zama Shugaban Real Madrid, bayan Mendoza ya aje mukamin.

A 1 ga watan Yuli 1996 ne Kocin kasar Italiyan nan Fabio Capello, ya isa Real Madrid don zama Koci. Inda ya nemo 'yan wasa don taya shi aiki. 'Yan wasan sune Seedorf, Suker, Mijatovic da kuma Roberto Carlos.

2 ga Fabrairun 1997 kuma daya daga cikin 'yan Real Madrid din nan, wanda ya dade yana bauta wa kwallo ya sami girmamawa da shugabancin kungiyar, a lokaci guda kuma ya zama mataimakin "FIBA".

Kamar yanzu a ranar 6 ga watan Maris na shekarar 2002 ne kulob din Real Madrid ya cika shekaru 100 daidai da kafuwa. Kuma a wannan ranar aka yi wata karawa a filin wasan kulob din da kungiyar nan ita ma ta kasar Sifen mai suna Deportivo La Coruna, a gasar nan ta La liga, inda kulob din ya sami nasara a kan abokin karawarsa da ci 2 da1. Wannan nasarar ta karawa bukin cikar kulob din shekaru 100 armashi, wanda har hakan ta sa ake kiran kulob din da ya fi fice a karni na 20 (Best Club of the 20th Century).

A kuma ran 15 ga watan Mayu 2002 ne, Real Madrid ta sake daukar kofin zakarun kasashen Turai, wato (European Champions) wanda shi ya kai yawan adadin daukar wannan kofi nata sau 9. Inda ta lallasa abokiyar karawarta ta kasar Jamus, Bayern Leverkussen da 1 da 2, inda Raul da Zidane, suka jefa kwallo daya-daya. Wanda hakan ya kawo adadin cin da Madrid ta yi wa wannan kulob a wasan karshe sau biyu.

Duk wannan ya faru ne bayan Real Madrid ta sami nasarar doke manyan abokan adawarta kamar Barcelona da kuma Bayern Munich. Wannan shekara na daga cikin shekarun da Real Madrid ba za ta manta da su ba a harkar kwallon kafa.

A 30 ga watan Agustan 2002 ne, Real Madrid ta sake samun wani gagarumin ci gaba, lokacin da ta ci kofin da ta taba rasawa a Bernabeu wato "Europe Super Cup" wanda ta ciwo a Monaco bayan ta doke Dutch Feyenoord, a wasan karshe. Roberto Carlos ne ya ci kwallo ta farko, van Hooijdonk da Guti, duk sun jefa kwallaye dai-dai, inda aka tashi wasan da ci 3 da 1.

A wasan Real Madrid ta nuna kwarewarta matuka, inda ta tafi da kofin, wanda ta rasa a shekarar 1998 da kuma 2000, a hannun Chelsea da Galatasaray. Don haka suka ce kofinsu ne ya dawo gida.

A kuma 31 ga Agustan 2002 din ne Ronaldo ya iso Real Madrid, wato bayan Luis figo ya zo a 2000, kuma Zinedine Zidane a 2001, wanda ya zama na ukun manyan 'yan wasan duniya da ya taka kasa a Santiago Bernabeu a karkashin Shugaban Real Madrid Florentino Perez. Bayan wata yarjejeniya da aka yi tsakanin Inter Milan, wadda aka cimma ran 31 ga watan Augustan 2002, wadda ita ce ta mai da Ronaldo ya zama dan wasan Real Madrid.

Dan wasan, wanda shi ne ya fi cin kwallo a gasar cin kofin duniya wanda aka yi a 2002 ya sami riga mai lamba 11. Kuma ya fara yi wa Real Madrid wasa a ran 6 ga Oktoba na 2002. Ronaldo ya fara wasa ne da kimanin mituna 64 da fara wasa, inda ya jefa kwallo a raga da kimanin mintuna 64. Wato minti daya kenan da shigarsa fili.

Ba kawai nan Ronaldo ya tsaya ba,sai da ya jefa kwallo ta biyu da kimanin minti 78 da fara wasa, wanda hakan ya sa Real Madrid ta sami nasara kan abokiyar karawarta Alaves da ci 5 da 2. A biyo mu bashi ba mu gama ba.

Komawa babban shafinmu                   Komawa saman wannan shafin