Za mu fara raba magani kyauta In ji Shehu Giant
Daga Umar Abubakar
An bayyana cewa a kwanan nan ne Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa za ta fara raba wa al’ummarta magunguna a dukkanin asibitocin da ke Karamar Hukumar kyauta. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Karamar Hukuma, Alhaji Shehu Ahmad Giant a sa’ilin da yake tattaunawa da DILLALIYA a ofishinsa da ke Magajin Gari.
Shugaban ya bayyana cewa dan tsaikon da aka samu wajen fara aiwatar da sabbin ayyuka yana da nasaba ne da jinkirin da aka samu tun daga gwamnatin Tarayya wajen sa hannu a kan kasafin kudi na bana.
Ya kara da cewa, “yanzun kam alhamdulillahi Shugaba ‘Yar’aduwa ya sa hannu a kan kasafin kudin, kuma mu ma har mun je Majalisa, inda muka kare namu kasafin kudin da muka tura mata, domin ta amince, ta kuma ba mu izinin fara aiwatar da ayyuka kamar yadda muka shirya tun farko. Don haka kwanan nan ne jama’armu za su fara gani a kas.”
Shugaban, wanda yake kuma shi ne Shugaban majalisar shugabannin Kananan Hukumomi ta nan jihar Kaduna ya yi tsokaci kan irin gudummawar da shugabannin suke bai wa talakawansu, wanda a mafi yawan lokuta talakawan ba sa la’akari da su. Nan ne ya ba da misalin yadda shigabannin suka dauki nauyin biya wa duk wani manomi sama da Naira 3000 a kan kowane buhun taki a daminar bana. Shehu Giant ya ce sun dauki nauyin sayo kowane buhun taki a kan sama da Naira 5000, a sa’ilin da su kuma za su saida wa manoman jihar a kan Naira 2000 kacal. Ya ce wasunsu sun biya wa manoman sama da Naira Miliyan 80, wasu 90, wasu 100, duk dai gwargwadon yawan manoman da ke yankinka.
Har ila yau Shugaban ya ce ba su tsaya a nan ba, a kwanan nan ne ma kuma za su fara raba wa yaran Karamar Hukumar da ke makarantar firamare littafai kyauta domin karfafa wa shirin gwamnatin jihar na ganin kowane yaro ya sami ilimi.
An yaba wa Shugaban Karamar Hukumar Chikun
Daga Umar Abubakar
Muddin al’amura suka ci gaba da tafiya a haka, to kuwa babu shakka nan ya zuwa 2011 wannan Karamar Hukumata za ta habaka. Wannan yana daga cikin jawabin da Shugaban jam’iyyar PDP a Karamar Hukuma Chikun, Alhaji Garba Mai Taki Buruku ya yi a sa’ilin da yake tattaunawa da DILLALIYA a kwanakin baya a nan Kaduna.
Alhaji Garba Mai Taki ya yaba kwarai da salon mulkin Shugaban Karamar Hukumar, Hon. Madami Garba Madami, musamman ta fuskacin samar da zaman lafiya a Karamar Hukumar ta hanyar janyo daukacin ’yan Karamar Hukumar a jika da kuma yadda yake kokarin hada kansu baki daya.
Shugaban ya kuma siffanta Garba Madami a matsayin mutum mai kwazo da kuma aiki tukuru, wanda ya ce su kam sun yi dace a wannan Karamar hukuma tasu ta Chikun. Yana mai cewa lallai kamar yadda jama’a suka fara gani nan ba da jimawa ba lamurra za su kara kyautatuwa a wannan yankin.
Ya kuma nemi jama’ar yankin da su karba kiran Shugaban na ci gaba da zaman lafiya da kuma bai wa shugabannin cikakken goyon baya domin kara samun ci gaba a yankin da ma jihar Kaduna baki daya.
Shugaban kuma ya dauki dogon lokaci, inda yake yaba wa Gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Muhammad Namadi Sambo, a bisa irin kamun ludayinsa wajen tafiyar da sha’anin gwamnati. Musamman ma yadda ya ya mai da hankalinsa kacokaf wajen warware dukkanin matsaloli da kuma abubuwan da da suke damun jama’ar jihar ta Kaduna. Da kuma yadda ya sakar wa Kananan Hukumomi mara suna tafiyar da sha’anunnukansu ba tare da ya sa masu baki ba, a inda kuma yake sakar masu kasonsu ba tare da ya kwange masu komai ba.
A nan ne Shugaban ya nemi daukacin al’ummar jihar da su bai wa Gwamnan da gwamnatinsa goyon baya, domin ta sami nasarar aiwatar da kyawawan manufofinta. Ya kuma yi wa Gwamnan godiya kan irin mukaman da Gwamnan ya bai wa ’yan asalin Karamar Hukumar ta Chikun.
Burinmu kankare wa mata da matasa talauci
-Hon. Fati Ibrahim
Haifaffiyar lardin Zazzau, Hon. Fati Ibrahim ’yar boko, gogaggiyar ’yar siyasa, kuma Shugabar kungiyar nan mai zaman kanta mai suna WUSLEK. Kungiyar da ta shahara wajen koyar da sana’o’in hannu kala-kala ga mata da matasa ba tare da sun biya ko sisi ba. Ta bayyana wa DILLALIYA manufarta da kuma dalilinta na kafa wannan kungiyar cikin wata hira ta musamman a gidanta da ke unguwar Wusasa Zariya.
Inda ta fara da cewa kan abin da ya shafi dalilinta na kafa wannan kungiyar, “ka san ni ’yar siyasa ce, kuma a yau mutane da yawa sun dauka cewa ’yan siyasa makaryata ne. Don haka ni ko a lokacin da nake yakin neman zabe, abin da nakan gaya wa jama’a shi ne ko na ci zabe kuma ko ban ci ba, ko da siyasa ko babu siyasa, kuma ko ta hanyar kungiya ce ni a shirye nake da in yi abin da na tabbata zai zama taimako a gare su, kuma ga shi mun cika wannan alkawarin.”
Hon. Fati ta kuma ce, “babu shakka na yi ayyuka da yawa wanda ko su wadanda ma aka zaban kila ba su yi kamar su ba. Farko na je na samo wata gudummawa daga Amerika, wacce da ita na zo na fara gina azuzuwa guda biyu, daya a bangaren mazauna musulmi, daya kuma a bangaren mazauna kiristoci, dukkan su dai a nan mazabata.”
Ta ci gaba da cewa, “daga nan muka shiga tara mata da matasa muna koya masu sana’o’i kala-kala da nufin ganin mun kore masu zaman banza da kuma zama cikin talauci, ta yadda za su zama masu dogaro da kawukansu. Muna kuma koya masu sana’o’in hannu ne kama daga yadda ake yin sabulu da yadda ake rina kayayyaki da kuma yadda ake yin ababen makwalashe kamar su kek da sauransu, ta yadda ko da ba ka da ‘oben’ za ka iya ka sayi kalanzir ka yi a risho. Ga kuma dinke-dinke duk mun koya masu su, da kuma saka. Kai har ma da yadda ake yin ado, duk mun koya masu. Ta yadda idan mace ce za ta san yadda za ta adonta kanta, ta yadda babu yadda za a yi Maigida ya ga wata a waje wacce za ta iya dauke masa hankali ta hanyar wannan adon. Tunda yake ka san da ma nine nake shugabancin kungiyar masu dinke-dinke da sake-sake irin na zamani ta nan reshen Abuja (Fashion Designers Association Of Nigeria Abuja Chapter), don ni ina son kowane lokaci in ga mata sun fito ne a matansu, yadda suke ta hanyar adonsu da tsaftarsu, kai har ma da tarbiyyarsu, ta yadda duk addinan nan guda biyu sun nuna mana muhimmancin wannan. Duk muna koya ma mata wannan, muna ma koya masu tsaftace gidajensu.”
Sannan Hon. Fati t ace, “ta bangaren matasa kuma, su muna koya masu zane-zane ne, tunda ka san ni ma abin da na koya kenan. Muna koya masu yadda za su yi katuna kamar na lokacin sallah ko lokacin kirsimati ko na aure da sauransu. Har da wasu abubuwan sha’awa na gyaran daki. Na samo kwararru a wannan fannin na ajiye a gida, wanda a duk sati, ba ma ko wane wata ba, suna zama su koya masu akalla sau biyu. Yanzun haka ma har wasu da yawa sun sauke karatun nasu.
A Zamfara, waye me gaskiya a zaben cike gurbi?
Daga Shu’aibu Samaru
Zamfarawa sun yi ta sanya idanu a kan abin da yake faruwa da abin da zai faru ga siiyasar wannan kasa tamu mai suna Najeriya. Sanin kowa ne cewa siyasar wannan kasar ta sauya sabon salo, sai kuma abin da wannan matar ta zo da ita da kuma yadda ta sauya daurin zani a cikin kasuwa, ta kwance fari ta mai da baki, za ta sauya uba ne ko a’a?
Za ku yarda da ni cewa salon siyasar Najeriya a yanzu ba shi ne asalin dimukaradiyya ba, abin ya koma wani abu daban. Sai dai kuma ban san irin sunan da malamai da ’yan siyasa da masu mulki za su sanya mata ba, domin sune suka sauya mata alkibla, daga Gabas ta koma Yamma.
Jihar Zamfara jiha ce wace take daya daga cikin jihohin Arewa, wadda ake alfari da ita bisa dalilai da dama, musamman idan aka dubi jama’arta. Kuma tana daya daga cikin jihohin da take bugun kirji da cewa, duk Najeriya ita ce kawai Mataimakin Gwamna ya gaji Gwamnansa. Bayan wannan kuma ita ce wadda ta fara kaddamar da shari’a, sa’annan sauran jihohi suka fara, a lokacin da ake ganin shari’a ba za ta yiwu ba a wannan kasar mai suna Najeriya. Don haka ba Najeriya kawai ba, a duniya baki daya idan aka gan ka ka ce daga Zamfara kake, to ka zama abin kallo.
Saboda irin wannan dalili ne ya sa ake ganin komai na Zamfara zai fita daban, tare kuma da gudanar da gaskiya da adalci ga ’yan jihar da kuma baki daya mazauna jihar. To, da yake muna cikin lokacin siyasa ne za mu so mu yi magana a kan abin da ya gabata kwanan nan a Karamar Hukumar Maru, wanda aka gudanar zabe, saboda rashin dan majalisarsu ta jiha, Bello Makau Ruwan Doruwa, Allah ya Jikansa.
Gwannan jihar Zamfara, Alhaji Mahmuda Aliyu Shinkafi, a matsayinsa na Shugaban al’umma, tun kafin zaben Kananan Hukumomi ya ce za su tabbatar an yi adalci, an bai wa kowa hakkinsa, duk da haka tsohon Shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Isma’ila Garkuwan Maradun, a zantawarsa da manema labarai tun kafin zaben Kananan Hukumomin ya ce bisa alama wannan gwamnati za ta yi adalci, kuma kamar yadda Mamuda ya ce, to suna fata idan lokacin zabe ya zo, to a yi adalci, a ba kowa hakkinsa.
Shi ma Shugaban jam’iyyar PDP na yanzu, Alhaji Namadi Ango, ya ce ya tabbata cewa sun tabbatar wannan gwamnati mai adalci ce, don haka suna fatan za ta yi adalci.
Shi kuwa Shugaban Hukumar zabe ta jiha, Alhaji Malami Aliyu ’Yandoto ya yi ta cika yana batsewa a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wani shiri na zakara. Wani ya tambaye shi ko za su yi adalci? Sai ya ce, duk wanda ya ci za su ba shi. “Duk wanda ya ci zabe za mu ba shi.” Kuma ya kara da cewa, babu abin da zai ji tsoron sa a yanzu, don haka zai tabbatar an yi adalci.
A kewayawar da na yi a lokacin da aka yi zaben cike gurbin, na yi matukar mamakin abin da na ji, kuma na gani. Da yake ban fita da wuri ba, rumfa ta farko da na je, abin da na fara cin karo da shi shi ne wasu yara masu karancin shekaru dauke kuma da katunan zabe, masu dauke da shekaru goma sha takwas. Sai na ce, ai ko ba yanzu aka yi rajistan nan ba, to amma lokacin da aka yi rajista shekarunsu nawa? Sai na tambayi wani yaron sunansa. Na ce shekarunka nawa? Ya ce goma. Wani abin ban mamaki shi ne yadda wani dan majalisa mai tsaron wannan akwatin ya taso ya ce, wai yaron ba goma yake nufi ba, yana nufin goma sha takwas ne, wai mune ba mu ji ba.
Sai kuma wata mazabar da mukaje, muka iske ba a kawo akwati ba, sai karfe goma sha biyu. Aka ba su umurnin kara lokaci zuwa karfe biyar na yamma, maimakon karfe uku. A wannan mazabar ne na gamu da cincirindon matasa kusan ishirin suna gindin inuwa. Sai na tambaye su ko sun yi zabe? Suka ce a’a ba su yi ba. Na ce me ya sa ba su yi zabe ba? Suka ce sai an ba su kudi, su sun daina sana’ar banza. Na ce, to yanzu nawa za a ba su? Suka ce, yanzu ana ciniki ne. Sai na nemi jin ta bakin daya daga cikin su, suka ki yarda.
Wani abin ban mamaki, da na kara gaba zuwa Mayanci, sai ga yaran da ba su wuce shekara bakwai ba zuwa goma, suna zanga-zanga, suna cewa, “mu ba za mu yi zabe ba, sai an ba mu kudi.” Sai na kira wani yaro mai suna Sanusi na karbi katinsa na ga an sanya shekara goma sha takwas. Sai na ce, Sanusi me ya sa ba za ka jefa kuri’a ba? Sai ya ce, “ba zan jefa kuri’a ba sai an ba ni kudi.” Sai na ce nawa zan ba ka? Ya ce, ko nawa na ba shi, ko Naira hamsin ne, in ba shi in gaya masa inda zai jefa, ya je ya jefa.
Barin Mayanci ke da wuya, sai muka koma Maru. Maru garin banga! Ashe na je a daidai, domin na sami Malamin zabe ya fara jawabi, yana cewa, “wasu sun zo wajen nan sun jefa mana wasu takardun zaben da ba namu ba, don haka za mu juye akwatin mu tsince wanda ba namu ba.” Sai na ce, to kallo ya koma sama, an ce shaho ya dauki giwa. Ai sai na sami guri ina kallon yadda ake tsince gurbattatun takardun, kulli bayan kulli. Idan da zai kirga su, za su kai sama da dubu.
A garin Ruwan Dorawa kuwa abin, sawun giwa ne ya take na rakumi, domin dambacewa aka yi tsakanin Sanata da Minista. Lalle abin ya wuce wasan yara, duk wadannan abubuwa sun faru ne saboda zabe. To idan za mu yi tambaya a nan, sai mu ce shin wadannan abubuwa sun faru ne saboda a tsai da gaskiya? Ko kuma domin a gudanar da gaskiya? Shi Wakilin zabe na garin Maru, wanda ya ce an kawo shi ne daga Sakkwato, da na tambaye shi cewa ya yi, wallahi ya zo ne ya gudanar da aikinsa na zabe tsakanin sa da Allah, don kuma al’umma da jama’ar Najeriya.
To, idan gwamnatin Mamuda ta ce za ta gudanar da zabe bisa gaskiya da adalci, sa’an nan shi Shugaban zabe ya ce, zai gudanar da zabe bisa adalci, haka kuma Malamin zabe ya ce, zai yi tsakani da Allah. Haka kuma abin yake ga hukumar ’yan sanda. Su daman tun kafin zabe sun ce za su tsaya tsayin daka, don tsare rayukan jama’a. To, yanzu jama’a wanene mai gaskiya, tunda ga shi yanzu kowa yana kuka yana cewa ba a yi masa adalci ba?
Don Allah dan uwa Bazamfare ka yi wa kanka adalci, ka yi wa kanka tambaya, ka kuma ba kanka amsa, shin wanene yake da ikon yi wa jama’a rajista? Kuma wace doka ce ta ba da damar yi wa yaro dan shekara bakwai zuwa goma rajista? Kuma jama’a sai sun dauka cewa sanya manyan jami’an gwamnati a wajen zabe zai kawo adalci ne da gaskiya, to yaya aka yi Kwamishina yana zaune a kan idonsa a matsayin Wakili ya ce bai san lokacin da wasu suka jefa wasu kuri’u a akwatin ba, amma wasu sun gani? Anya kuwa ana so a kulla gaskiya?
Wani abin bakin ciki shi ne yadda za a ce manyan mutanen da suke zaune a Abuja a matsayin wakilai na jama’a, wadanda suka fito jihar da take shari’a, a ce Minista da Sanata su yi fada a gaban jama’a. Ko kuwa dukkansu suna fada ne don a tabbatar da gaskiya?
Lalle kam al’amarin zabe ya zama abin da ya zama. Anya jama’a suna so su gama da duniya lafiya kuwa? Wani sabon abin da ya gudana kafin zabe shi ne yadda gwamnati ta ware zunzurutun kudi Naira miliyan goma sha bakwai karkashin jagorancin Kwamishinan lamurran addini don raba wa Limamai da Ladanai domin su yi wa gwamnatin Mahmuda addu’a. Wannan shi ne ake kira kuskure, saboda tun kafin zaben Kananan Hukumomi, wasu ’ya’yan jam’iyar ANPP suke ta Allah ya isa cewa ba a yi masu adalci ba a wajen tantance dan takara. Wasu sun fito ta kafafen watsa labarai sun yi magana, kamar daya daga cikin ’yan majalisar jihar, Muttaka Rini, da Mai martaba Sarkin Zurmi, cikin jawabansa ga kwamitin tantance ’yan takara, cewa ya yi gwamnati da shugabannin jam’iya sun kira shi sun ce ga wanda gwamnati take so, shi ne Tafidan dauran. To, babu abin da za su ce dole su karba su yi biyayya, domin babu wanda yake ja da gwamnati, su kuwa talakawa babu abin da suke fadi sai “Allah ya isa!”
Anya kuwa ana so a haifa wa wannan jaririyar jiha da mai idanu? Kuma ta yaya idan an ciza a hura, ana sara ana duba bakin gatari? Domin ko babu komai an ce gani ga wane ya isa wane tsoron Allah. Saboda irin haka ne da abin ya yi yawa, jama’ar jihar Jigawa kafin zaben Kananan Hukumomi suka sauke Alkur’ani sau dari biyu da ishirin ga duk wanda ya yi almundahana. Sai ga shi bayan zaben cikin wata guda, gobara ta tashi, ta lashe kusan gidaje arba’in, annoba dai wata bayan wata. Kuma idan ba a manta ba Malamai sun ce Allah ba ya barin addu’ar wanda aka zalunta. Matukar ka zalunci mutum ya ce, Allah ya isan masa, to babu makawa Allah zai isan masa, ko ba jima ko ba dade.
Abin da nake so a lura da shi a nan shi ne yadda kowane bangare ya nuna zai yi bakin kokarinsa na za a yi adalci, amma wani abin bakin cikin shi ne yadda wasu suka gudanar da abin shi ne kamar jihohin da babu shari’a, babu addini. Duk wata jihar da babu addini, duk abinda suka yi daidai da su ne, amma ba jihar Zamfara ba, inda ake 99.9% musulmi ne kuma ake da’awar Musulunci.
Babu siyasa a rabon hatsi a Zamfara
-Tukur Jekada
An bayyana cewa babu bambancin siyasa a rabon hatsin da Gwamnatin jihar Zamfara ta gudanar. Wannan batu ya fito ne daga bakin mai ba Gwamna shawara a kan harkar wayar da kan jama’a, Alhaji Tukur Jekada Birnin Tudu, lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa.
Wannan kalami na Tukur Jekada ya biyo bayan zargin da jama’a suke yi ne na cewa ba kowa gwamnatin ta bai wa hatsin da ta raba wa talakawa ba, sai idan kai dan siyasa ne kuma dan jam’iyyar ANPP.
Alhaji Tukur ya ce wannan zargi ne kawai wanda ba shi da tushe bare makama. Don haka ya ce, “Wannan zargi ne kawai wanda wasu suke yi domin batanci ga wannan Gwamnati, bayan ga shi jam’iyyun adawa suna yabawa da yadda wannan Gwamnati take tafi da al’amuranta,” in ji shi.
Jekadan ya kara da cewa, wannan rabon hatsin an kafa masa kwamiti ne, saboda haka su ’yan kwamitin suke baje hatsin duk mai bukata, sai ya zo don ya saya. Ya ce, hatsin na al’umma ne gaba daya, don haka tunda an riga an kammala zabe ko kowa da kowa na gwamnati ne. Don haka Gwamnati za ta yi wa al’umma aiki ne gaba daya.
Tukur Jekada ya nemi masu yada jita-jita da masu neman mulki ido rufe da su ji tsoron Allah kuma su sanya tsoron Allah cikin zuciyarsu, kuma su zo a tafi tare da su a yi wa al’ummar jihar Zamfara aiki tunda Gwamnatinsu ba ta kyamar kowa, kuma a shirye take ta tafi da kowa don gina wannan jihar da al’ummarta.
Za mu fafata da Kananan Hukumomi 34 na jihara Katsina
-Shugaban Karamar Hukumar Sabuwa
Daga Husaini Ibrahim
Shugaban Karamar Hukumar Sabuwa da ke jihar Katsina, Alhaji Shafi’u Madawaki Inono, ya bayyana cewa majalisarsa ta yi shiri tsaf don fafatawa da dukkannin Kananan Hukomomi talatin da hudu da ke fadin jihar.
Shugaban Karamar Hukamar ya bayyana haka ne a wajen rantsar da kansilolin Karamar Hukumar da aka yi kwanan baya.
Madawaki Inono, ya bayyana cewa al’ummar Karamar Hukumar ne suka zabe su, don su zama jagororinsu kuma su rike masu amanar dukiyoyinsu da rayukansu da kuma ciyar da wannan Karamar Hukumar gaba. “Saboda haka dukkan Kansilan da bai zo da niyyar cika wa al’ummar yankinsa irin wannan alkawari ba, ya zo ne don ya gina kansa ba al’ummarsa ba, to lallai ina mai shaida masa da cewa ya tattara komatsensa. Mazabarsa su turo wani,” in ji shugaban Karamar Hukumar.
Alhaji Shafi’u ya kara da cewa “Don dukkan wanda yake nan ina mai shaida masa cewa ayyukan da muka yi a karon farko, to lallai yanzu za mu yi ninkinsu da taimakon Allah. Don mun yi shirin fafatawa da kowace Karamar Hukumar da ke jihar ta Katsina.”
A bangaren ayyukan ci gaba daga kowane sashi na Karamar Hukumar, wanda ya hada da bangaren lafiya, ilimi, jin dadin jama’a da aikin gona wanda a yanzu haka suna da katafaren wurin kiwon kifi a wanana Karamar Hukumar. Ya bayyana cewa yanzu haka jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, za ta rinka amfani da wannan wajen kiwon kifin nasu don koya wa dalibanta yadda ake yin kiwon kifin zahirinsa. Ya ce wannan ba karamin abin alfahari bane ga Karamar Hukumar tasu.
Da ya koma bangaren tsaro, Shugaban ya bayyana cewa wannan Karamar Hukuma tasu ta shirya tsaf don fafatawa da bata gari da kuma Da’u fataken dare. Ya ce an raba motoci, babura da kekuna ga jami’an ’yan sanda da na ’yan sintiri don taimaka masu wajen yakar wadannan ’yan ta’adda.
A karshe da yake godiya a madadin wadanda aka rantsar, mataimakin Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Abdurrahaman Sirajo Damari ya bayyana cewa dukkan kudurin da Shugaban Karamar Hukumar yake da shi na ci gaban Karamar Hukumar su ma a shirye su ke su ba shi goyan baya fiye da zatonsa don ganin Karamar Hukumar Sabuwa din ta ci gaba.
An rantsar da kansilolin Karamar Hukumar Funtuwa
Daga Husaini Ibrahim
Shugaban Karamar Hukumar Funtuwa, Hon. Muntari Dandutse ya rantsar da ’yan majalisarsa masu ofisoshi a Karamar Hukumar. Da yake jawabi jim kadan bayan rantsar da ’yan majalisar, Shugaban Karamar Hukumar ya bayyana cewa wadanda zai rantsar Allah ne ya ba su wannan mukami ba don sun fi kowa ba.
Da kuma ya koma kan wadanda ya rantsar din, Shugaban ya bayyana masu cewa wajibi ne a kansu da su zage damtse wajen ci gaban wannan Karamar Hukuma tasu. Ya kara da cewa, dukkan wanda ba burinsa bane ya ga an samu ci gaba a wannan Karamar Hukumar, to lallai kam ba zai zauna tare da su ba. Don haka ya ce yadda suka faro ayyukan ci gaba ta kowane fanni a wannan Karamar Hukuma tasu, to a wannan karo ma rubanyawa za su yi.
Ya ce wannan ce tarbiyyar da Shugaban kasa, Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa ya ba su ta yin aiki tukuru. Ya kara da cewa wannan tarbiyya da aka ba su ta zama jini da tsoka a jikinsu. Don haka ya ce shi ma magajinsa Gwamna Ibrahim Shehu Shema a kullum kudurinsa shi ne ci gaban wannan jiha tasu, ya ce kodayaushe a kan haka suka dora su.
“Don haka yadda muka mori shugabanni masu son ci gaba ya zama mana wajibi mu bi su, don bin su shi ne zai kawo mana ci gaba a wannan Karamar Hukuma tamu,” in ji Dan Dutse Funtuwa.
Wadanda aka rantsar sun hada da Mansur Abu Maigishi, a matsayin mai kula da mulki da kudi, sai Hon. Mas’udu Dodo mai kula da Ma’aikatar noma, da Abdulhadi Shehu Mai kula da Ma’aikatar ayyuka da gidaje, sai kuma Abdullahi Maitukku sashen walwala da jin dadin jama’a, da kuma Barista Yazidu Abdullahi Ma’aikatar lafiya.
Babban bako kuma Uba ga jam’iyyar PDP, Alhaji Babajo Ibrahim ya gargadi shugabanni da su ji tsoron Allah su ba mara da kunya kamar yadda Shugaban Karamar Hukuma ya zabo su su taimaka masa yadda za a ciyar da wannan Karamar Hukuma gaba. Ya ce kamata ya yi su dage da yin aiki tukuru don ganin an sami ci gaba fiye da yadda bai zata ba.
Da hadin kan matasa ne za mu sami ci gaba a Maska
In ji Hon. Kabir Sani
Daga Husaini Ibrahim
Kansila mai wakiltar mazabar Maska cikin Karamar Hukumar Funtuwa jihar Katsina, Alhaji Kabir Sani Maska, ya bayyana cewa da taimakon matasa ne za su sami damar ciyar da mazabarsa ta Maska gaba.
Kansilan ya bayyana cewa ba don taimakon matasa ba da suka ga cancantar sa suka fito da shi a matsayin dan takararsu, ba mai wakiltar su a majalisar Karamar Hukumar Funtuwa, kuma suka kasa suka tsare, suka tabbatar ya ci zabe, to da ba shi bane a matsayin Kansila.
Don haka ya bayyana cewa wannan ya nuna cewa lallai da hadin kan matasa ne dukkan abu ke tabbata. “Don haka ina fatan za su ba wannan Gwamnati hadin kai a karkashin jagorancin Hon. Muntari Dan Dutse don ganin an samar wa al’ummar mazabar Maska da abubuwan more rayuwa. Wannan shi ne kudurin Shugaban Karamar Hukumarmu a kodayaushe. Kuma akan haka ne na ke kira ga Shugaban Karamar Hukumarmu Hon. Dandutse a kan yadda al’ummar Maska suka dauke shi tamkar wanda aka haifa a garin Maska, ayyukan da yake da kudurin yi mana, to muna roko da ya nunka su. Wannan kuma abu ne mai sauki a gare shi,” in ji Kansila Kabir Sani Maska.
Mu bayin al’ummar Karamar Hukumar Dandume ne
In ji Hon. Abdulkadir Muhammad
Daga Husaini Ibrahim
Shugaban Karamar Hukumar Dandume da ke cikin jihar Katsana, Hon. Abdulkadir Muhammad, ya bayyana cewa su kansu wadanda al’ummar Karamar Hukumar suka zaba don zama shugabanninsu tun daga kansa har zuwa Kansiloli zababbu da kuma wadanda aka nada dukkansu bayin al’ummar Karamar Hukumar Dandume ne.
Shugaban ya ce saboda al’ummar Karamar Hukumar sun dora masu nauyin tafiyar da wannan Karamar Hukumar.
Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake rantsar da Sakatarensa da Kansiloli masu ba shi shawara a garin Dandume hedikwatar Karamar Hukumar Dandume.
Hon. Abdulkadir Muhammad, ya kuma bayyana cewa ya zama wajibi ga al’ummar Karamar Hukumar su taya su da addu’a kodayaushe don addu’arsu ita ce ginshikin ci gabansu baki daya.
Shugaban ya kuma gargadi masu yi wa shugabanni mummunar addu’a da cewa bai kamata ba, kuma ba adalci bane, don haka babu riba a rika yi wa shugabanni mummunar addu’a. Don haka ya yi kira da a rika yi masu kyakkyawar addu’a.
Don haka ya kara da cewa “Ba mu da wani jinkai ko isa, don daga gare ku muke kuma ba mu da wani arziki sai na jama’a, ba za mu raina ku ba, ba za mu ji kyashin ku ba, kuma ba za mu guji shawarar waninku ba. Kodayaushe kofarmu a bude take don samun shawarwari daga gare ku,” in ji Hon. Abdulkadir Muhammad.
Haka kazalika kuma ya yi kira ga dukkanin ’yan jam’iyyun da ba PDP ba da su zo su ba da hadin kai a tafi tare da su. Ya bayyana cewa yanzu sun zama daya za su yi aiki babu bambancin siyasa.
Da ya koma bangaren wadanda aka rantsar, Shugaban ya bayyana cewa dole wajibi ne su zo ofis don yi wa jama’a aiki kamar yadda shi ma kullum yana ofis matukar yana gari. Ya ce Allah ya ba su gwarzayen ma’aikata masu son ci gaba, don haka za su yi aiki da su don ganin sun sami ci gaba a wannan Karamar Hukumar ta Dandume.
Amadadin wadanda aka rantsar, Sakataren Karamar Hukumar, Alhaji Lawal Isiyaku Tumburkai ya bayyana cewa lallai za su ba mara da kunya, kuma za su yi aiki tukuru don ganin an samu ci gaba a Karamar Hukumarsu.
Gwamnatin PDP za ta taimaka wa matasa
-Hasan Daudawa
Wannan ita ce tattaunawar da Wakilinmu na jihar Katsina ya yi da Shugaban matasa na jam’iyyar PDP na kasa reshen Arewa maso yamma, Alhaji Hasan Muhammad Daudawa. Ga yadda hirar tasu ta kasance;
DILLALIYA: Ranka ya dade za mu so ka fada wa masu karatunmu takaitaccen tarihinka.
HASAN DAUDAWA: Sunana Alhaji Hasan Muhammad Daudawa. An haife ni a cikin garin Daudawa da ke Karamar Hukumar Faskari a jihar Katsina. Kuma na yi makarantar firamare da sakandare a nan garinmu, sannan na tafi makarantar kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya. Har yanzu ni dalibi ne a cikinta, kuma ina da mata da yara.
DILLALIYA: Shin me ya ba ka sha’awa yadda kake matashi haka ka famtsama fagen siyasa?
HASAN DAUDAWA: Alhamdu lillahi, ni siyasa ta zama mani gado ne, don na sami Mahaifina yana siyasa, domin shi aminin Shugaban kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa ne. Sun yi zama da shi a Daudawa. Suna siyasa tare, don haka na dau fagen siyasa na tsunduma cikinta duk da na yi ayyuka da dama, amma na aje na shiga siyasa. Kuma a yanzu cikin ikon Allah ya sa na shiga jam’iyya mai nasibi, ba ma a fadin kasar nan ba a Afirka baki daya, jam’iyyarmu ta zama uwa ta siyasar Afirka baki daya ga sauran jam’iuyu, wato jam’iyyar PDP.
DILLALIYA: Jihohin da kake shugabanta suna da dimbin matasa marasa aikin yi, kuma sun taka rawa sosai don ganin jam’iyyarku ta kai gaci, shin kowane irin shiri kake da shi don ganin an sama masu aikin yi?
HASAN DAUDAWA: Ita jam’iyya har kullum ba ita ce Gwamnati ba. Ita ce uwa kuma duk inda aka ce uwa da da, sai dai ba da shawara. Kuma ita kanta shari’a ta ba da dama idan danka ya zama baligi, ya kamata ka kira shi ka ba shi shawara da nasiha, babu bugu a ciki, babu tursasawa.
Ita jam’iyya uwa ce ta masu shugabanci, don haka mu kam sai ba da shawara ga masu shugabanci tun daga Kansila har Shugaban kasa muna ba su shawara da kuma tsarin da ya kamata a yi.
Mun tura wa Gwamnatocinmu yadda za a taimaki matasa, domin tsakani da Allah matasanmu na cikin wani hali. Inda nake wa jagoranci za ka ga matasanmu ba su da sana’a. Don haka yanzu mun dauki wasu matakai na samun ci gaba, kuma Gwamnatoci sun fara ba mu hadin kai don sama wa matasa sana’ar hannu.
Misali daga jihata, wanda yanzu haka Gwamna Ibrahim Shehu Shema ya kafa Ma’aikatar koyon alli da fenti, wanda a yanzu haka kusan matasa sama da dubu biyu ne za a yaye daga wannan ma’aikata. Sannan ya umurci kowace Karamar Hukuma da ta fara aiwatar da koyar da wannan sana’a don taimakon matasa.
Wannan fentin da ake koya wa matasan ya amsu, don yanzu dukkan irin fentin da ake bukata ana samun sa a Katsina, ba sai ka je waje ka sawo ba. Wannan ma ya sa Gwamnan jihar Kaduna, Namadi Sambo ya turo matasa daga jiharsa don koyon yadda ake wannan fentin.
Kowace jiha akwai irin nata salon taimaka wa matasa. Don haka nake kira ga masu hannu da shuni da su taimaka su kafa irin wadannan kamfanoni don taimakon kansu da ’ya’yansu. Don kauce wa fadawar matasa daba da kungiyoyin ta’adda.
DILLALIYA: To, a karshe meye fatanka ga yankin da kake wa jagoranci?
HASAN DAUDAWA: Kullum dan Adam ya kamata a ba shi hakuri. Dukkan abin da mutum ya nema bai samu ba sai ka ce masa yayi hakuri. Zan ba da shawara ga matasa. Yawancin matasanmu sun yi karatu ba su samu aikin yi ba. Insha Allahu Mai girma Shugaban kasa zai bullo da yadda za a taimaki matasa. In ka duba shi a kullum yana son ya ga ya samar wa matasa abin yi da rayuwa mai sauki. Don yanzu mutane suna ta kuka suna cewa suna shan wahala.
To, mu mun san waye Umaru Musa Shugaban kasar Nijeriya, don ya shugabance mu shekara takwas, don haka jinkirinsa alheri ne, babu hadari a cikin jinkirinsa don in ya fito da ayyukan alheri mutane sai sun sha mamaki. Don gyara in aka zo yin sa, sai an sha wahala, barna ce ba ta da wahala.
Me Gwamnatin Dakingari ta gada a jihar Kebbi?
Bayan haye siradin kotun daukaka kara da Gwamnatin Alhaji Sa’idu Usman Nasamu Dakingari na jihar Kebbi ta yi, wanda ke cike da ban mamaki da kuma rudu al’ummar jihar suka zura ido don ganin ina wannan gwamnati ta surukin shugaban tarayyar Nijeriya za ta sa gaba.
Wasu na yi wa gwamnatin kallon wata Gwamnati ce, wadda Gwamnanta ke tsaye da kafafunsa don ganin ya cika alkawuran da ya yi wa al’ummar jihar yayin yakin neman su zabe shi da ya yi kokacin yakin neman zabe a bara.
Wasu kuwa na yi wa Gwamnatin Nasamu kallon wata Gwamnati ce wadda ke cike da jami’an Gwamnatin da ta gabata ta Alhaji Muhammadu Adamu Aliero. Don haka suke ganin Gwamnatin a matsayin tsohuwar Gwamnatin da ta gabata. Saboda irin wannan kallo da suke yi wa wannan Gwamnati ya sa suka fice daga duk wani al’amarin da ya shafi wannan Gwamnati.
Sai kuma ’yan adawa da suka fito daga jam’iyyu biyu, wato ANPP da kuma DPP, wadanda dukkansu adawa suke yi bilhakki da wannan Gwamnati.
Adawar ANPP da Gwamnatin Dakingari ta samo asali tun lokacin da tsohon Gwamnan jihar, Alhaji Muhammadu Adamu Aliero ya fice daga cikin jam’iyyar tare da wadanda ya kira magoya bayansa, inda suka nufi jam’iyyar PDP, yayin da mataimakinsa tare da wasu da suka kira kansu ’yan jam’iyyar ANPP na asali suka kasance tare da wannan jam’iyya har zuwa lokacin da aka yi babban zabe, wanda ya kai ga samun nasarar Gwamna Dakingari. Tun daga nan aka sa zare tsakanin Sanata Adamu Aliero da jama’arsa da kuma ’yan jam’iyyar ANPP, musamman dan takarar Gwamnanta Sanata Faruq Bello Bunza.
Wani abu da ya fi daukar hankali a siyasar jihar Kebbi ita ce gabar siyasar da ke tsakanin Sanata Adamu Aliero Garkuwan Gwandu da amininsa, Alhaji Abubakar Malam Shettiman Gwandu. Wadannan mutane abokan juna ne, tun kafin zuwan siyasa suke tare a gidan kwastam.
Shi kansa Shettiman na Gwandu ya sha bayyana cewa shi ubangidan Adamu Aliero ne. Domin, a cewarsa shi ya fara dauko Sanatan ya nuna shi ga al’ummar jihar don a zabe shi Sanata a Kebbi ta tsakiya. Ya ce bayan an zabi Adamu Aliero ne zamanin siyasun UNCP, sai Allah ya yiwa Shugaban kasa na wancan lokaci Janar Sani Abacha rasuwa, don haka sai aka rushe siyasu.
Abubakar Malam ya kara da cewa bayan an rushe siyasun ne, tsohon Gwamnan ya dawo ya roke shi a taimaka a mayar da shi aikin kwastam, amma sai shi Shettima din ya hana shi bisa hujjar cewa ya yi hakuri tunda Allah ya sa ya kammala aikinsa lafiya, to ya jira siyasa ta dawo ya yi takara.
Haka ta kasance a tsakaninsu har aka dawo da siyasa a zamanin Gwamnatin Abdussalam Abubakar, inda shi Adamu Aliero ya roki Shettima kan ya bar shi ya yi takarar Gwamna maimakon tsayawa takarar Sanata. Inda Shettiman wanda a wannan lokaci mataimakin shugaban kwastam ne na kasa, ya goya wa Adamu Aliero baya har ya yi Gwamna sau biyu a jihar ta Kebbi.
Yayin da ya shaida wa Adamu Aliero cewa zai aje aikinsa na kwastam don dawowa gida ya tsaya takarar Gwamna kamar yadda suka yi alkawari tuntuni, Gwamnan ya amince da wannan magana. Amma bayan ya dawo gida, sai tsohon Gwamnan ya dauko yaron su (Dakingari) shi ma daga gidan kwastam ya tsayar da shi takarar a jam’iyyar ANPP a wancan lokaci. Ganin haka ya sa dole Shettiman Gwandu ya fice daga jam’iyyar ta ANPP ya koma DPP don tsayawa takara, saboda cin amanar da aka yi masa.
Bayan ficewar Shettiman ne, sai kuma Janar Muhammadu Magoro Galadiman Zuru, ya fito takara a jam’iyyar PDP. Ganin cewa shi tsohon Gwamnan ba zai kai labari ba, sai ya yi tukun-tukun don a bar shi ya koma jam’iyyar ta PDP, kuma a ba shi damar kawo dan takarar Gwamna, don a ganinsa idan har ya ja da Janar Magoro da PDP, to dan takararsa ba zai kai labari ba. Don haka sai ya ture Magoro ya kawo Dakingari ya tsaya takarar da duniya ke kallon ta a matsayin takarar da ta saba wa tsarin dokokin zaben kasar nan. Yayin da wasu ke cewa sam ba haka bane Shugaba Obasanjo ne ya tura masa karensa na EFCC ya firgita shi. Don haka ya ga ba shi da zabi face komawa gidan na Obasanjo don ya sami kubuta daga cizon wannan kare.
Ko ma dai me ake ciki, gabar da ke tsakanin Gwamnatin Alhaji Muhammadu Adamu Aliero da ’yan adawa za a iya cewa wannan Gwamnatin ta gaje ta. Domin kuwa kusan duk jami’an waccan Gwamnatin suna cikin wannan Gwamnati. Don haka wannan Gwamnati ta Alhaji Sa’idu Usman Nasamu, za a iya cewa har yanzu ba a san inda ta sa gaba ba, shin za ta tafi tare da ’yan adawa da suke adawa da tsohon Gwamnan don ciyar da jihar gaba, ko kuwa ita ma za ta dora ne daga inda waccan Gwamnatin ta tsaya? Saboda haka al’ummar jihar gaba daya yanzu sun zura ido ne don ganin inda Gwamnatin Nasamu ta sa gaba.
Kasar nan ana fama da rashin abinci
In ji Danliman
Daga Abdullahi Tumburkai
“Kasar nan na cikin wani hali na rashin abinci da kuma tsadar kayan masarufi na yau da kullum da talaka ya saba amfani da su don ganin rayuwarsa ta ci gaba.” Wannan kalami ya fito ne daga bakin Alhaji Dk. Fara’u Danliman mai sayar da shadda na kasuwar Kaduna.
Don haka ya yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta taimaka wa talakan kasar nan don rage masa halin radadi da kuma yunwa da rashin abinci da ake fama da shi a kasar nan.
Danliman ya bayyana cewa kamata ya yi Gwamnati ta fito da hatsin da aka saya aka aje domin irin wannan lokaci don sayarwa talaka cikin farashi mai rahusa. Ya ce, yin hakan zai rage wa talaka radadin da ake ciki a wannan lokaci da ya kira na rashin tabbas ga talaka.
Ya ce duk da kowa ya san wannan hali ba kasar nan ce kadai ke fama da shi ba, hali ne da ya zama ruwan dare, amma Gwamnati na da irin rawar da ya kamata ta taka don ganin wannan hali bai kai na intaha ba.
Ya kuma yaba wa Gwamnatin tarayya bisa umurnin da ta ba da na a shigo da shinkafa ta Naira biliyan tamanin. Ya ce wannan abu da Gwamnatin ta yi, ta yi shi a lokacin da ake bukatar sa.
Don haka ya jaddada rokonsa ga Shugaban kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa da sauran Gwamnonin kasar nan da kuma shugabannin Kananan Hukumomi da su yi duk yadda za su iya don ganin an fita daga wannan bala’i da ya zama ruwan dare game duniya.
Ya ce “kamata ya yi shugaba Umaru Musa ’Yar’aduwa ya taimaka ya ga an shigo da kayan abinci da kuma na masarufi kasar nan. Idan aka yi haka, to na tabbata za a sami saukin wannan hali da ake ciki.”
Daga nan ya yi kira ga dukkan bangarorin Gwamnati uku da su taimaka wajen samar da takin zamani da sauran kayan aikin gona don a sami damar noma isasshen abinci a kasar nan. Ya ce Allah ya hore mana kasar noma da kuma al’umma masu kwazo, don haka idan har an sami isasshen takin zamani ba abin da zai hana manoma noma abin da kasar nan za ta ci.
Daga nan Danliman ya roki al’ummar kasar nan da su ci gaba da yi wa kasar nan addu’a don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
An fara zaman makoki na yini uku a China
An fara zaman makoki na yini uku a China don juyayin mutanen da girgizar kasar nan ta rutsa da su, mako guda bayan mummunar girgizar kasar da ta auku a China. A ranar Litinin 19 ga Mayu, 2008 aka fara zaman makoki na kwanaki uku don tunawa da wadanda suka rasu a wannan bala´i daga Indallahi. An sauko da tutoci, sannan an soke gudanar da duk wasu shirye-shirye da sauran bukukuwa a cikin kasar har karshen zaman makokin.
Tun da sanyin safiyar ranar, sojoji sun yi maci zuwa dandalin zaman lafiya da ke birnin Beijing, inda kamar a duk fadin kasar aka sauko da tutar China zuwa rabin gora da misalin karfe biyu da rabi agogon China, wato daidai lokacin da girgizar kasar ta auku kenan a ranar Litinin ta makon jiya. Kasar ga baki kaya ta tsaya cak. An yi shiru sannan an yi ta buga jiniya tsawon mintoci uku, wato tsawon lokacin da kasa ta girgiza kenan wadda ta halaka mutane kimanin dubu 50.
Mutane ne dai sun fita kwansu da kwarkwatansu don nuna juyayinsu. Wasu ’yan kasar da suka hallara a dandalin don nuna alhininsu suka ce “ya kamata mu da muke raye mu yi juyayin wadanda suka rasa rayukansu musamman a wannan bala´i.”
Tutocin Jamus da na kungiyar Tarayyar Turai da ke a gaban ofishin jakadancin Jamus na daga cikin na ofisoshin jakadancin kasashen ketare da aka fara sauko da su yau da safe. Su ma kamfanonin ketare sun nuna zumuncinsu ga al´ummomin China. Yanzu haka reshen kungiyar agaji ta Red Cross a Jamus ya tura wani asibiti na tafi da gidanka inda yanzu haka aka kwantar da mutane 120. Sannan a tsakiyar wannan mako jiragen samansa biyu da wata tawagar likitoci za su isa yankin da bala´in ya auka ma.
Kawo yanzu a cikin Chinar kanta an tara kudaden taimako kimanin Yuro miliyan 800. Sannan wani shirin talabijin da aka gudanar jiya an tara karin miliyan 150, kamar yadda masu gabatar da shirin suka nunar.
Dukkan bangarori na al’ummar kasar sun taimaka. Wata dattijuwa cewa take "mu ma mun taimaka, kowa ya taimaka. Jikokinmu ne a cikin makarantun. Wannan bala´in dai ya shafe mu duka."
A halin da ake ciki, bala´in na girgizar kasar shi ne batu guda daya tilo a shirye-shiryen tashoshin talabijin kasar. Sun hada dai da hirarraki masu sosa rai da aka yi da dangin wadanda suka rasa ’yan uwansu, da hirarraki da ma’aikatan agaji likitoci da ma’aikatan jiya da kuma zantarwa da Shugaba Hu Jintao ya yi da wadanda suka tsallake rijiya da baya a wannan bala´i.
A yau din kuma Shugaba Hu ya mika godiyarsa ga dukkan kasashen da suka kai wa China dauki a wannan lokacin da take juyayin dubun-dubatan ’yan kasar da suka rasu a girgizar kasar.
Me ke sa farashin danyen mai ya tashi?
A karon farko cikin tarihi, gangar danyen mai daya ta kai dalar 123. Farashin man fetur na ci gaba da tashin gwauran zabo a kasuwannin duniya, inda a yanzu ganga daya ta kai dalar Amurka 123.
Wannan shi ne karon farko da gangar danyen mai daya wato lita 159, ta kai dala 123 a cikin tarihin hada-hadar makamashi ta duniya.
Tunda jimawa masana a game da kasuwar man fetur suka yi hasashen wannan tsada, wadda a cewar su ganga daya na iya kaiwa ga dala 200, muddin ba a dauki matakan da suka dace ba tunda sauran wuri, kamar yadda David Wyss na kamfanin cinikin makamashi mai suna Rating Standard Poors ya nunar.
Ya ce, mun jima muna sa ido a game da tafiyar farashin, kuma mun san a rina.
Tun shekaru shida baya farashin ya fara yin sama, inda sannu a hankali ya kai dala 100.
A shekara ta 2002 an sayi gangar danyen mai daya tsakanin dala 19 zuwa 21.
A shekarun gomomi na 1980, an fuskanci karancin man fetur wadda ta sa farashi ya karu da kashi 8 cikin dari.
Sai dai bambanci da na wannan karo shi ne cewa tsadar man na wakana a daidai lokacin da Amurka ke fama da karayar tattalin arziki da kuma tazara da Euro ke ci gaba da bai wa dalar Amurka, wadda da ita ne ake gudanar da dukkan cinikayyar da ta shafi man fetur a manyan kasuwannin duniya.
“Wadannan matsaloli biyu sun jawo illoli masu yawa ga tattalin arzikin sauran kasashen duniya,” in ji Anthony Grisanti na kamfanin GRC-Energy: Kamar mahaukaciyar guguwar Hurricane, matsalar kariaar tattalin arzikin Amurka ta bazu a duniya.
Rikicin da yake wakana a yankin Gabas ta tsakiya ya kuma kara hau da wannan farashi.
Bayan rikicin na Gabas ta tsakiya musamman ma takon sakun da aka shiga tsakanin Iran da kasashen Turai da Amurka, dillalan man fetur sun dangata wannan mumunar tsadar mai da tashe-tashen hankula a yankin Neja-Delta da ke Nijeriya, inda kungiyar MEND ke ci gaba da kai hare-hare ga bututun mai na kamfanonin da ke hakar man fetur a wannan yanki.
A nata gefe, kungiyar kasashe masu albarkatun man fetur, wato OPEC ta ce ba za ta kara yawan man da take hakowa ba, daukar wannan mataki bisa dukkan alamu zai kara ta da hankula da rudamin fuskantar wani yanayi, inda amfani da man fetur zai gagara mai dan karamin karfi.
Kungiyoyin da suke fafutakar kare muhalli sun nunar da cewa hanya daya tilo ta kawo karshen matsalar, ita ce ta yawaita amfani da makamashi ta hanyar sarrafa hasken rana, tsirai da kuma iska.
Abin da ya sa na koma PDP
-Malam Hadi Balarabe
Kodayake Malam Hadi Balarabe asali dan jam’iyyar PDP ne, har ma ya ci gajiyar jam’iyyar a lokacin da jam’iyyar ta kafa gwamnati a karon farko a jihar Katsina karkashin jagorancin Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa, lokacin da aka ba shi shugabancin Hukumar ilimin firamare ta jihar, sai dai daga bisani Malamin ya canza sheka, inda ya koma jam’iyyar ANPP. A nan ma ya zama jan wuya, inda ya yi wa ’yan takarar jam’iyyar shugabancin kamfe kama daga Nura Khalil a karon farko da Abu Ibrahim a karo na biyu. Sai a wannan lokaci angulu ta koma gidanta na tsamiya, wato Malam Hadi ya koma jam’iyyar PDP. A cikin wannan tattaunawar da ya yi da Wakilinmu Salisu Tukur Gaiwa, Malamin ya rarrabe tsakanin zare da abawa a kan dalilansa na sauya matsayi. Mai karatu idan ka karanta wannan hirar zuwa karshenta za ka fahimci dalilan komawar Malam Hadi Balarabe cikin jam’iyyar PDP.
RUDANI A JAM’IYYAR ANPP
Abubuwa da yawa sun faru a cikin siyasar kasar nan. Matsaloli na shugabanci kusan a ko’ina, musamman a cikin ita jam’iyyar ANPP wadda na bari. Sad da muka taho jam’iyyar ANPP muna fuskantar zabe, an samu wani irin rudani, wanda kusan ma ba a iya bayyana yadda yake. Ana cikin wannan rudani har zuwa sauran kwanaki goma a yi zabe. Ya zama an sanya wa mutane ido kowa yana yin yadda ya ga dama.
Lokacin da aka yi zaben fitar da dan takarar Gwamnan jihar Katsina an samu rudani wanda wadanda suka zo lura da zaben daga matakin kasa sun yi abin da suke ganin shi ne ya fi dacewa gare su, daga bisani aka gano cewa ba haka ya kamata su yi ba. To, wannan ne ya sa sashen kamfen na Alhaji Abu Ibrahim suka rubuta koken cewa ba su yarda da yadda aka gudanar da zaben ba. Uwar jam’iyya ta kasa ta duba ta kuma ga cewa ba a yi abin da ya kamata ba. To, kuma a daidai wannan lokaci, lokaci ya kure wanda za a sake wani zabe saboda haka aka tsaya a kan cewa Alhaji Abu Ibrahim ya kasance dan takarar jam’iyyar sakamakon wani taro da aka yi a Kaduna.
Wannan ya sa bangaren Nura Khalil ya tafi kotu yana kalubalantar wannan mataki da uwar jam’iyya ta dauka, ya kuma ci gaba da kiran kansa dan takara. Wannan ya sa ’yan jam’iyya suka kasa rarrabe wanene ma tukun dan takarar na hakika.
Wadannan matsaloli duk sun samo asali daga sakancin ita jam’iyyar da ta kasa kafa kafafuwanta kasa ta ce ga dan takararta. A haka fa ne aka shiga wancan zabe.
Bayan an yi wannan zabe abin da ya faru ya faru, kuma sai aka rika ganin laifin wasu mutane a kan faduwa zaben. Alhalin tsarin da aka shigo da shi zaben ne gaba dayansa ba ya da inganci.
Wannan ne ya sa da farko na yanke shawarar gara mutum ya sa ido ya yi ta kallon abin daga nesa tunda dai zagon kasa da ake yi wa jam’iyyar daga shugabancin jam’iyyar yake tasowa. Musammam ma abubuwan da suka faru bayan zaben Shugaban kasa, inda uwar jam’iyya da dan takararta aka yi ta samun takun saka a tsakani. Yau wadannan su ce kaza, gobe wadancan su ce kaza. Sai na ga komai mutum yake son ya yi wa jam’iyyar, shugabancinta ba irin wanda za a yi wa biyayya bane.
BA RASHIN HADA KAI DA AC YA KADA ANPP BA
Wasu na ganin kamar rashin hada kai da jam’iyyar AC ya sa ANPP ba ta kai labari ba, amma ni ba ni da wannan ra’ayin, domin a gaskiyar magana jam’iyyar AC a wancan lokaci ba wata jam’iyya bace. Abin da ya faru, tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya tsaya kai da fata sai ya ga ya tsaya takarar Shugaban kasa. Jam’iyyar PDP kuma ta ki ba shi wannan damar. Iyakar dalilin kafa jam’iyyar AC kenan. Domin kawai biyan bukatar wani babba mai son takara, ba wai wata manufa bace takamaime da akidu suka samar da jam’iyyar. A wancan lokacin, a hakikanin magana jam’iyyu masu karfi guda biyu ne – ANPP da PDP.
BAMBANCIN ANPP DA PDP
Da ma a PDP nake, na fito daga cikinta, kuma bayan shekaru biyar da ’yan watanni na sake dawowa cikinta. Daya daga cikin dalilaina na komawa PDP shi ne ban yi nufin barin siyasa ba. Inda na yi nufin barin siyasa, da sai in ce na bar ANPP kuma in dawo in yi zamana. To, amma sad da na bar ANPP ban riga na ce ga jam’iyyar da zan koma ba. Ko a AC wasu sun tuntube ni, a PDP ma na samu gayyata. To, amma ni ma’aunin da na yi amfani da shi shi ne maganar shugabanci.
A ANPP muna zargin jam’iyyar PDP da yadda ake gudanar da lamurra, to amma in ka lura ka kwatanta da shugabanci na ANPP akwai zargi mai tsanani. Amma shugabancin PDP na yin abubuwa ne da jama’arsu baki daya domin ganin jam’iyyar ta yi nasara. Amma a ANPP ana yin abubuwa ne wani lokacin ma don a karya ita jam’iyyar, inda shugabannin jam’iyya ke yin abubuwa domin karya jam’iyyarsu. Me ya sa mutum zai ci gaba da zama a irin wannan jam’iyyar?
To, bayan na bar ANPP ranar 10 ga watan Oktoba, shekarar da ta gabata, sai na zo na zauna watanni biyu kafin in tafi PDP, bayan na yi la’akari da wadansu abubuwa. Ita kanta PDP an samu canje-canje cikinta. Kuma in dai mutum zai yi adalci zai ce eh, akwai canjin da aka samu a cikinta. Musamman yadda mai girma Gwamnan jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema ke tafiyar da jagorancin jihar Katsina. Misalin da zan ba da a nan shi ne yadda ya tallabo matasa yake neman su amfana kuma kyakkyawan amfani daga tsare-tsaren gwamnatinsa. Da ma kuma wannnan abin ne jama’a ke so.
Daga cikin tallabar matasan da ya yi, banda batun fenti da alli da ya sa matasan suka raja’a wajen koyo da sarrafawa, har wasu matasa 50 ya kashe wa makudan kudade don su koyo walda ta zamani wadda daga bisani za su iya aiki a kamfanonin jiragen sama da na ruwa. Yanzu haka ma kamfanoni na zawarcin su.
Ga batun karin albashi wanda ya tsaya tsayin daka cewa sai dai idan kowa zai samu har da Malaman makaranta. Wannan ya sa Malaman makaranta da a da ake bari baya sun ji dadi, haka ma dukkan ma’aikata.
Ga kashe kudin makaranta da ya yi, abin da zai sa kowa a jihar ya shaida da lagwadar dimokradiyyar gwamnatinsa tunda yake kusan kowa a jihar ba zai rasa yaro daya ko biyu da ke makaranta ba. Ba ma kudin makaranta ba, har ma da na jarabawa.
Ka ga wadannan abubuwan ba ’yan PDP kawai aka yi mawa ba, a’a kowa da kowa aka yi mawa, ba tare da la’akari da jam’iyyar da ya fito ba.
To, kuwa a duk lokacin da gwamnati ta raja’a ga aikin da zai shafi rayuwar kowa da kowa, to ya kamata a goyi bayan irin wannan gwamnatin, domin ta ci gaba da irin wannan aikin.
Hatta jihar Kaduna sai da ta zo jihar Katsina ta yi nazarin shirin koya wa matasa fenti da alli, aka kuma debi mutane daga nan suka je can suka horar da matasansu yin fenti da alli. Daga karshe ma wajen kaddamar da shirin har sai da Mataimakin Gwamnan jihar, wanda ya wakilci Gwamnan jihar, ya rubuta a kan allo cewa “mun gode jihar Katsina,” saboda jin dadin shirin.
Ka ga kenan jihar Katsina ta ciri tuta a sanadiyyar gwamnati mai alkibla. Wadannan kadan ne daga cikin dalilan da suka sa na yanke shawarar shiga jam’iyyar PDP, tunda ko ba komai gwamnatin da ta kafa na yin aikin da jama’a ke so kuma suke yabawa.
Komawa Shafin Farko
|