Labarin rayuwata
-Mataimakin Gwamnan Kebbi
Batun ’yan Nijeriya wadanda suka bautaw a kasar nan bilhakki, wadanda suka yi aiki wurjanjan na sama da shekaru talatin, to in ka sami irin su Alhaji Ibrahim Aliyu, Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi, za a iya bayyana shi a matsayin uba, wanda ya yi aikin Gwamnati a bangarori daban-daban na kasar nan.
Kafin kotun daukaka kara ta Kaduna ta tabbatar da zabensu, shi da Gwamnan jihar, Alhaji Sa’idu Usman Nasamu Dakingari, makonni uku da suka wuce, Alhaji Aliyu a wata hira da ya yi ya bayyana tudu da gangaren da ya bi har ya kai ga wannan matsayi. Ga abin da yake cewa: “Na fara karatun bokona ne ina da shekaru 6. Na kuma fara ne da makarantar firamare ta kauyenmu. Daga nan na wuce kwalejin Gwamnati ta Sakkwato, wadda ake kira Nagarta College a yanzu. Bayan na kammala sai na tafi jami’ar Ahmadu Bello Zariya, inda na sami digiri biyu a lokaci guda, wato na Tarihi da kuma sanin sha’anin Gwamnati.
Bayan na kammala, sai na fara aiki da tsohuwar Gwamnatin jihar Arewa maso yamma, inda na yi aiki na dan wani lokaci kafin in wuce jami’ar Ife, wato jami’ar Obafemi Awolowo a yanzu, inda na yi babban digirina kan sha’anin mulki. A 1974, aka nada ni Sakataren Hukumar kula da sanya wutar lantarki.
“Bayan nan, na canza aiki zuwa hukumar zabe ta kasa (FEDECO) a 1982. Daga nan kuma na zama Sakataren Hukumar kula da Kananan Hukumomi da kuma tallafa wa dalibai.
“A 1987 aka nada ni Janar-manaja na kamfanin samar da kayan noma na jihar Sakkwato. Daga nan na zama babban Sakatare, inda na yi aiki a Ma’aikatu da dama a bisa wannan mukami na babban Sakatare, kafin na zama Sakataren Gwamnatin jihar Sakkwato.
“Lokacin da aka kirkiro jihar Kebbi, na zama Sakataren Gwamnatin jihar na farko (SSG). Bayan mika mulki ga zababbiyar Gwamnatin farar hula ta farko, sai na wuce makarantar koyon sanin makamar mulki da ke Kuru a Jos, (NIPSS), inda na yi karatu har na sami lambar nan ta mni. Daga nan kuma Allah ya sa aka kara kira na na sake zama SSG a jihar Kebbi.”
A dai ci gaban da ya samu, mataimakin Gwamnan ya ci gaba da cewa, “Babu shakka mun sami horo da kuma tarbiyya, wanda hakan ya taimaka mani kwarai wajen samun nasara a rayuwata. Na sami tarbiyya yadda ya kamata daga iyayena, musamman an horar da ni da in kasance mai saukin kai ga jama’a, kamar yadda mahaifina ya horar da ni. Babana Shugaban al’umma ne, Kakana kuwa Mai gari ne. Babana ya kasance jarumi ne, ya sanar da mu yadda za mu kasance ’yan uwan juna masu kaunar juna. Zan iya tunawa cewa lokacin da ina rami mutane ba sa son yin abin assha. Saboda tsoron kada a ce suna abin da ba daidai ba. Zan kuma iya tuna cewa na kasance mai taimaka wa iyayena a gona da kuma gida, wanda hakan ne ya taimaka mani a yau.”
Me ya sa Alhaji Aliyu ya shiga cikin harkokin siyasar kasar nan tsundum kuma ya yake kallon ita wannan siyasar ganin ya fito ne daga cikin gidan da yake da tarbiyya ta kwarai da kuma yadda ya aiwatar da ayyukan Gwamnatinsa cikin nasara? “Yayin da aka kafa jam’iyyar PDP ina daga cikin wadanda aka kafa ta da su.” Ya ba da amsa nan take.
A cewarsa, “Ina daga cikin wadanda aka kafa jam’iyyar PDP da su, na zama memba a kwamitin amintattu na jam’iyyar har zuwa 2001 lokaci da aka nada ni Kwamishina don wakiltar jihar Kebbi a Hukumar kidaya ta kasa. Na bar nan 2007, yayin da jam’iyyata ta zabe ni domin in zama dan takarar mataimakin Gwamna. Zan bayyana karara cewa yadda na gudanar da aikin Gwamnati da na yi, ya taimaka mani matuka wajen fuskantar kalubalen siyasa.
Duk da cewa na san siyasa na da wani yanayi wanda ya dan takura ni matuka, amma saboda irin gogayyar da muka samu ta fuskacin aikin Gwamnati. Kodawane lokaci ina tabbatar da cewa abubuwa sun tafi yadda ya kamata. Ina bakin kokarina kan haka kuma insha Allah wata rana sai labari. Dukkan abubuwan da muke yi yanzu share fage ne na wannan dimokradiyyar tamu. Abubuwa za su daidaita nan gaba.”
Me mataimakin Gwamna ke shirin yi nan gaba tunda shekaru sun fara yin nisa?
“Ina fatan ganin na sami ’yar gonar da zan yi kiwon shanu da kuma noman kifi a cikinta. Wanda hakan ne nake ganin zai sa na zama mai yin wani abu har zuwa karshen rayuwata. Kuma ina fatan koma wa makarantar addinin Musulunci don kara samun ilimin Kur’ani.”
Shin mataimakin Gwamna na da lokacin yin karatu duk da wasu harkoki da ke gabansa?
“Eh, ka yi gaskiya, matukar na sami dama, ina son yin karatu. Ina karanta littattafai da daman gaske da kuma Kur’ani. Sannan kuma ina yin wasan ‘Hockey’ da ‘squash,’ amma ina fatan in dan yi wasan ‘badminton’ da kuma ‘swimming.’”
“Abin da na fi so a rayuwata sune ’ya’yana. Ina son su sosai kamar yadda kowane uba yake son ’ya’yansa. Gaba daya ina da ’ya’ya maza takwas da kuma mata shida. A cikin su hudu sun sami damar kammala karatunsu, sannan biyu za su kammala bana, sannan sauran wasu na firamare, wasu kuma sakandare.
Wanene mataimakin Gwamna ke fatan ya zama gwaninsa? Ina son in zama kamar wadannan muhimman mutane sune; Alhaji Tafawa Balewa, Ahmadu Bello, Obafemi Awolowo, Nnamdi Azikiwe da kuma Aminu Kano.
Matsa Nan
|