www.dillaliya.freeservers.com

Sanata Abu Ibrahim:
Abu, mai abin badawa!

Daga Abdullahi Tumburkai

Idan ana maganar siyasa ta hakika, siyasar taimaka wa jama’a, siyasar ba da gaba ba, siyasar ganin darajar wadanda suka zabe ka, ba wai kawai a jihar Katsina ba a kasar nan baki daya in aka kira sunan Sanata Abu Ibrahim, to sai kawai a yi fatiha a shafa.

Tun lokacin da ya shugabanci jam’iyyar PDP a jiharsa ta Katsina, jama’a ke kallon sa a matsayin wani bango abin jingina ta kowace fuska, tun daga taimakon jama’a da kuma sanin ya kamata na wannan dattijo.

Bayan Gwamna Umaru Musa ’Yar’aduwa ya kore shi daga wannan jam’iyya a shekarar 2003, dattijo Abu Ibrahim ya tsaya takarar Sanata don wakiltar mazabar Funtuwa (Katsina ta kudu) a majalisar dattawan Nijeriya a karkashin jam’iyyar ANPP.

Abu Ibrahim halinsa na alheri ya bi shi, domin kuwa a wannan zabe na shekara ta 2003 ne ya kayar da Shugaban masu rinjaye na ita wannan Majalisar dattawan tarayyar Nijeriya, wato Sanata M.T. Liman.

Cin wannan zabe da Sanata Abu Ibrahim ya yi ya kara masa kwarin gwiwa matuka don ganin ya share wa al’ummar yankinsa hawaye bisa matsalolin rayuwa da suka addabi talakawan mazabarsa.

Shigarsa majalisa ke da wuya sai ya fara da abin da ya kai shi, domin shi ne ya kawo dokar nan da aka sa wa hannu don magance matsalar zaizayar kasa da ake fama da ita musamman a arewacin kasar nan.

Don ganin al’ummarsa sun amfana da ayyuka kuwa, Sanatan ya gyara tare da gina burtsatse 274 a dukkan fadin mazabarsa don rage wa al’umma halin da suke ciki na rashin ruwan sha ingantacce.

Daga nan sai aka sami bullar annobar amai da gudawa a garin Maska da ke Karamar Hukumar Funtuwa, Sanatan ya taka rawar gani ga wadanda wannan annoba ta shafa, domin kuwa ya sayi magani na sama da Naira miliyan guda, aka raba wa wadanda wannan annoba ta shafa. A Karamar Hukumar Danja da Kafur ma an sami wannan matsala, inda Sanatan ya sayo magani na kimanin naira miliyan biyar, aka bayar da shi ga kyauta wadanda wannan annoba ta shafa.

Wani abin burgewa shi ne dukkan wadannan abubuwa da Sanata Abu ke yi yana yin su ne da kudin aljihunsa. Don haka ma wasu ke yi masa kirari da cewa “Sanata Abu mai abin badawa.”

Ba wai kawai nan Abu Ibrahim ya tsaya ba, sai da ya samar wa da matasa cibiyar koyon sana’o’i don dogaro da kai, wanda marigayi Sanata Yari Gandi na jihar Sakkwato ya wakilci shugaban majalisar dattawa, Sanata Ken Nnamani a wajen bukin bude wannan shiri, wanda aka yi tare da taimakon hukumar samar da ayyukan yi ta kasa, NDE.

A bangaren makarantu kuwa Sanatan ya gina tare da kuma gyara makarantu da daman gaske a wannan mazaba tasa. Ya gina azuzuwa biyu a makarantar sakandare ta mata da ke garin Bakori. Ya gina azuzuwa biyu a makarantar sakandare ta garin Musawa duk da kudaden aljihunsa.

Ya gyara makatantu a kusan dukkan Kananan Hukumomin da suke karkashin mazabarsa da suka hada da ta garin Sabuwa, makarantun islamiyya guda biyu a garin Funtuwa, gyaran masallatai da makabartu da sauran ayukan da wannan rubutu ba zai iya ambatowa ba.

Wajen tallafa wa jama’a kuwa Sanatan na daya daga cikin Sanatoci uku da aka yi a majalisar Dattawa wadanda ba su taba yin mako biyu ba ba tare da sun zo mazabarsu ba don jin koken da al’ummarsu ke da shi.

Duk wani dan siyasa da wanda ba dan siyasa ba da ya kamu da rashin lafiya a fadin jihar ta Katsina ko kuma aka yi masa rasuwa, to wajibi ne ka ga Sanata Abu Ibrahim a wajen don gaishe da mara lafiya din ko kuma yin ta’aziyya ga wadanda aka yi wa rasuwa.

Akan sami wasu ’yan siyasar da tsananin gaba da wadanda suka saba masu ko kuma suke adawa da su. Abu Ibrahim ba haka yake ba, domin kuwa ya goya mutane da daman gaske a siyance kuma yanzu ba sa tare da shi. Amma idan suna da wata bukata suka rasa sukan zo su same shi kuma ya yi masu.

Duk da cewa Sanatan bai sami damar zama Gwamnan jihar Katsina ba kamar yadda al’umma jihar suka kada masa kuri’arsu, Sanatan na nan yana ci gaba da abubuwan da ya san al’ummar jihar za su amfana da su.

Wani abu da ke kara wa Sanata Abu kima a idanun jama’a shi ne ra’ayinsa. Domin duk wanda ya san Sanatan ya san shi da ra’ayi daya ne. Baya magana biyu, domin duk abin da ya fada maka, to ba zai taba canza shi ba komai dadewa. Irin wannan ra’ayi nasa ne ya sa shi zama inuwa daya da janar Muhammadu Buhari. Domin kowa ya san cewa Janar mutum ne mai gaskiya kuma ba ya tafiya da wanda ba shi da gaskiya.





Matsa Nan