www.dillaliya.freeservers.com

Matambayi…
Da gaske ne akwai mota mai amfani da lantarki maimakon mai?

Taswirar DuniyaBayani game da mota mai amfani da lantarki a maimakon man fetur ko gas da aka sani To, babu shakka da akwai motar da aka kera da ke amfani da lantarki, to amma fa ba wai ta dogara ga lantarkin ne zalla ba, domin kuwa tana hadawa da mai kamar sauran motoci.

Wannan nau'in mota ita ce Turawa suka yiwa lakabi da kirar ‘HYBRID’, wanda ke nufin wani abu da aka hada shi ta amfani da fasaha fiye da daya wanda zai taimaka masa wajen yin aiki.

To, ita dai wannan mota, kamar yadda aka gani a bayanin farko, ta dogara ne da nau'in makamashi biyu - lantarki da kuma mai, saboda da gamayyar fasaha da aka tsara a cikin injinta, wanda zai ba ta damar yin hakan. Haka kuma injinta karami ne ba kamar sauran ba.

Yadda take hada wadannan makamashi guda biyu dai shi ne, a duk lokacin da aka ta da ita, tana tashi ne da mai, to amma da zarar ta fara gudu ta bukaci karin wuta maimakon mai da za ta kara sha, sai ta koma kan karfin lantarki da batirinta ke samarwa. A takaice dai mota ce da ke da karancin amfani da mai a kan sauran motoci.

Kamfanonin kera motoci dai sun fuskanci wasu matsaloli da suka tilasta masu tunanin samun mafita wajen ci gaba da kera motoci. Matsalar farko ita ce ta ci gaba da tsada ko kuma hauhawar farashin da mai ke yi da kuma batun gurbata yanayi da hayaki yake yi.

To, sakamakon matsalar farko ta farashin mai ne masana ta fannin kimiyya da kuma masu masana'antun kera motoci suka shiga binciken hanyoyin samar da mai iri daban-daban da mota za ta iya amfani da su. Daya daga cikin fasahar da suka iya ganowa ita ce ta yin amfani da lantaki da batir da kuma hayaki ko kuma wutar da mota kan samar a lokacin da aka tashe ta.

Babu shakka gano wannan fasaha ta taka rawar gani domin kuwa ta taimaka masu wajen jifan tsuntsu biyu da dutse guda. Domin kuwa bincike ya nuna cewa baya ga rashin shan mai da wannan nau'in mota take da shi, tana da saukin gurbata yanayi a kan sauran motoci. Bugu da kari kuma wannan nau'in mota an mata tsarin sifa na keta iska yadda za ta iya gudu sosai. Wato karama ce mara nauyi. Tayoyinta karfafa kuma matsakaita.

To, kamfanonin motoci irin su Toyota, Honda da Ford na daga cikin wadanda suke kera motar da ke amfani da lantaki da mai a tare. Kiyasin da aka fitar na kasuwar motoci a shekara ta 2004 ya nuna cewar daga cikin motoci miliyan 17 da aka sayar a shekara guda 80,000 kirar Hybrid ne. Da kuma shekara ta zagayo a 2005 an gano cewar bukatar irin wadannan motoci ya karu, inda adadin wadanda aka sayar ya kai kimanin 200,000. Zuwa shekarrar bana kuwa wato shekara ta 2008, adadin da aka sayar ya kai 400,000. Kuma har yanzu tagomashinta sai kara gaba yake yi.

Wane gini ne mafi tsawo a duniya?

To, tarihin dogayen gine-gine dai za a iya bin diddiginsa tun shekaru daruruwa ko ma a ce dubbai da suka wuce, lokacin da makera da kuma maginan asali suka fara yin kokarin gina dogayen gine-gine Mahadi ka ture. Kama dai daga dalar giza ta kasar Misra, har zuwa kasaitaccen ginin hasumiyar birnin Dubai, wanda yanzu haka ake tsaka da ginin ta.

Tun shekaru da dama da suka gabata, lokacin da aka fara samun ci gaba a bangaren fasahar gine-gine, masana ilimin zanen gine-gine suka rika zana da kuma kirkirar samfuri daban-daban na dogayen gine-gine, kama dai daga ofisoshi na Ma'aikatu yadda za su dauki Ma'aikatu da dama, har ya zuwa otal-otal da asibitoci da kuma gidajen tarihi. Har ila yau kuma sakamakon juyin zamani da yanayin muhalli da kuma bukatun al'umma ya sa tsarin dogayen gine-gine yake kara zama ruwan dare gama duniya.

To, idan kuwa ana batun gini mafi tsawo a duniya sai a ce, ginin hasumiyar birnin Dubai da ke hadaddiyar daular Larabawa, shi ne gini ma fi tsawo yanzu haka a duniya, kuma kasancewar ba a kammala shi ba tukuna, ana kara bayyana shi da cewa shi ne gini mafi tsawo da aka sani zai tabbata a nan gaba. Inda yanzu haka shi wannan gini ya kai hawa 145 kamar dai yadda maginan suka bayyana. Kuma in banda shi, ba bu wani gini a doron duniyar nan da ya kai hawa 145.

An dai fara gina wannan hasumiya ta birnin Dubai a ranar 21 ga watan Satumba, 2004. Kuma ana sa ran kammala shi a shekara ta 2009. Idan aka kammala shi, ginin zai kasance yana da sama da hawa 160.

Burj Dubai shi ne gini mafi tsawo a duniya

Wane Shugaban kasa ne mafi karancin shekaru a duniya?

Shugaban jamhuriyar dimokradiyyar Congo, Joseph Kabila, shi ne Shugaban kasar da ya fi karancin shekaru a tsakanin shugabanin kasashen duniya. Joseph Kabila, ya hau mulki ne bayan mutuwar mahaifinsa, Laurent D. Kabila tsohon Shugaban ’yan tawayen Congo, wanda dogarawansa suka kashe shi a watan Janairu na shekara ta 2001.

Bayan mutuwarsa da kwanaki goma, aka zabi dansa Joseph Kabila a matsayin shugaban jamhuriyar dimokradiyyar Congo.

Joseph Kabila shugaban jamhoriyar dimokradiyyar Congo an haife shi ne a ranar 4, ga watan Yuni, na shekarar 1971. Yau shekarunsa 37 kenan da haihuwa, kuma duka-duka bai shige shekaru 30 da haihuwa ba ya zama Shugaban Congo.

Joseph Kabila shi ne babban dan Shugaba Lawrent Kabila, daga cikin 'ya'yansa goma. Joseph Kabila ya zama zababben Shugaban Congo a shekara ta 2006. Gwamnatocin kasashen yammacin duniya kamar su Amurka da Faransa, tare da wasu Gwamnatocin kasashen Afirka da suka hada da Afirka ta kudu, da Angola, sun yaba tare da bayyana goyon bayansu ga zaben Jospeh Kabila a matsayin Shugaban Congo, musamman yadda suka cimma moriyar wasu harkoki na kasuwanci na miliyoyin dala, a zamanin Gwamnatinsa.

Shugaban na Congo, wanda ya sami horonsa na aikin soji daga kasar Sin, ya kasance dumu-dumu cikin ’yan yakin sari-ka-noke a zamanin da kasar ta sha fama da yake-yake. Joseph Kabila ya taimaka wa mahaifinsa, wajen kifar da Gwamnatin Mobutu Sese Seko, a shekarar 1997, bayan da Gwamnatin Mobuto na Zaire a wancan zamani ta shafe shekaru fiye da 20, tana shugabanci.





Matsa Nan