www.dillaliya.freeservers.com

Budaddiyar Wasika Ga Babban Mai Shari'a Na Nijeriya

Rokon a yi adalci
Prince Ibrahim Dandodo Laka

Idris KutigiNa rubuto wasiku da yawa zuwa ga ofisoshinka a kan wannan batun da nake a halin yanzu, amma ban sami amsa ba ko da sau daya. To ko ma dai me ke faruwa matsanancin halin da nake a ciki a yau ya ci gaba da faruwa, tamkar kai ka ce ni ba dan Nijeriya ba ne ko kuma ba ni a karkashin inuwar tsarin mulkin Nijeriya da ya tanadi yin shari'ar gaskiya, 'yancin walwala, addini, damar mallakar dukiya da abin da ya shafi komawa ga dakunan shari'a da dai makamantansu. Abin dai da nake son ka tabbatar da shi shi ne, idan har wannan ukuba da nake a ciki ta yi sanadiyyar mutuwata, to kada ka ce ba ka da masaniya, sai dai ka ce ka zabi ka yi biris da ita ne.

Na sha wahala ne saboda na zabi in kai kukana kotu, kuma a karshe kotun ta tabbatar min da hakkina, wanda hakan bai yi wa wasu daga cikin 'yan uwan Babban Mai Shari'a dadi a rai ba. Wannan hukunci da kotu ta yi sai ga shi kwatsam an ce an jingine shi ta wata hanya wacce za ta bai wa duk wani masanin shari'a ko harkokin yau da kullum mamaki. Kuma sai ga shi wai a yau ina cikin tsanani saboda kawai na yi aiki da wancan hukunci da kotu ta ba ni, kuma har ga shi ana tursasa ni kamar wani mai laifi.

Tashi biyu Alkalan kotunan majistare biyu (Alkalin kotun majistare ta 5,da Alkalin majistare ta 2 da ke Minna) suka sauke kansu da kansu a kan wannan shari'a saboda nuna son kai da suka yi a fili. Lauyana ya rubuta wa babban Mai shari'a, inda ya kai ma shi wannan kukan nawa, ni ma kaina na rubuta masa wanda kuma duk babu wani abu da ya wakana. Ganin wadannan rubuce-rubucen ba su yi komai ba ya sa na yanke shawarar na rubuto maka kai tsaye, wanda kuma a nan sai ga babban Mai shari'a yana ba ni amsa da kansa, inda yake ce mani wai wannan kuka nawa ba shi da tushe, duk kuwa da cewa ba shi na rubutawa ba, kuma bai amsa wanda na rubuta masa ba a can baya.

Wannan amsar da ya ba ni ta tabbatar da abin da ake zato, kamar dai sauran Alkalan majistirorin da suka nuna mani rashin adalci a can baya cewar su da suke wai su suna bin umurni ne daga sama. A sa'ilin da na kai karar Hukumar raya birane ta jihar Neja kan cewa suna fa daf da su rusa wa mutane muhallinsu da suka saya daga gare ni, babban Mai Shari'a bai amsa ba har sai da suka gama rushe-rushensu.

Abin mamaki kusan duk kararrakina shi da kansa yake dora wa kansa hakkin sauraron su, kuma hatta wadanda ma farko ya tura ga wasu manyan kotunan, duk sai da ya sake maido da su a gabansa. Na kai kuka a kan cewan da aka yi wai an jingine hukuncin da kotu ta ba ni bayan na bi duk hanyoyin da shari'a ta tanada, amma sam ba a ma yarda an tura wa kotun daukaka kara da ke Abuja takardun nawa ba.

To, in ma dai kamar yadda aka ce ne, an jingine hukunci, kuma an yi umurni da a sake shari'ar, inda abokanin jayyayan nawa suka nemi da a ba su sati biyu domin su kimtsa, yau ga shi sama da shekara kenan ba su iya gabatar da komai ba da nufin kare kansu daga wannan hukuncin. In da mu kuma muka ce, to tunda haka ne, muna neman kotu da ta kori wancan jingine hukunci da aka ce an yi, amma babu wani abin da kotun ta yi kawo yanzu.

A karshe dai ganin ba za a sami damar a tsare ni ba ta hanyar alkalan majistarori, sai aka shigar da wata karar da aka biyo ta gidan gwamnatin jihar Neja da ke Minna, wanda ta hakan ne ya kai ga har an kama ni. A nan ne babban Mai Shari'a ya kafa wata kotu ta musamman wanda babban rajistara da ke babbar kotun Minna yake shugabanta. Mu biyar ne aka gabatar kuma aka tsare mu nan take. Lauyana ya shigar da karar tabbatar da hakkin dan Adam, wanda kuma ya samu amincewa aka ba da umurnin a tsayar da dukkanin tuhume-tuhume aka kuma ba mu 'yancinmu na walwala, amma kuma suka yi biris ba su bi umurnin kotun da ke gabansu ba, sai suka ci gaba da tsare mu a gidan yari tamkar wasu masu munanan laifuka.

Ganin yadda wannan al'amari ya zama tamkar wasan yara ne ya sa ni da mutane biyu muka tsere daga hannunsu bayan mun shafe kwanaki sama da arba'in muna tsare. Tun kuwa wancan lokacin sauran biyun suna can tsare, yau maganar ta haura watanni bakwai kenan, suna kuma ci gaba da tsare su, ba tare da kuma sun gabatar da wata tuhuma a kansu ba. Kafin mu nemi 'yancinmu daga wancan babbar kotu wacce kuma ta ba mu kamar yadda tsarin mulki ya tanada kan abin da ya shafi hakkin walwala, mun gabatar da bukatunmu a rubuce da kuma baki na neman wannan kotun ta ba mu beli, amma abin duk sai ya ci tura, suka yi kememe suka hana ba tare da wani sharadi ba daga tsarin mulki.

A cikin irin wannan hali ne fa Babban Mai Shari'a ya ci gaba da gabatar da duk wata shari'a tawa a gaban kotunsa duk kuwa da yake shi kansa ya san ni ba zan halarci wani zama a kotunsa ba saboda rashin sikkan da nake da shi kan cewa zai yi mani adalci. A nan nake cewa tunda dai na lura abin da yake so kenan ni kam ba zan sake halartar wani zama a kotunsa ba, bari na bar shi da shari'un ya hadiye abinsa

Babu wani ma'aikacin Ma'aikatar Shari'a da yake son a gan mu a inuwa daya tare da shi ta fuskacin aiki, kai ko da ma ta fuskacin hulda haka nan kawai tsakanin ni da shi, saboda yadda suka ji shi kansa Babban Mai Shari'a din ya fada. Kuma duk wata takarda, matsawar tana da dangantaka da shari'ata, to tilas ne sai an kai masa teburinsa ya gani.

To, daga baya-bayan nan ma sai ga 'yan sanda sun zo har gidana da nufin wai su kama ni kamar yadda suka ce, wai na tsallake beli. Kai ka ce ba su san da umurnin Babbar Kotun tarayya da ta ba ni 'yancina ba. Ko kuwa umurnin Babban Kotun tarayyar ya zama umurnin banza ne a wurinsu, shi ne ba mu sani ba. Da suka ga ba za su iya kama ni ba, sai suka tsare motar hawata wacce a yanzu haka maganar nan da muke yi tana can hedikwatar 'yan sandan ciki da ke Minna.

A yanzu na fahimci cewa rayuwata ta shiga cikin hatsari daga lokacin da na rubuto maka kukana dangane da Babban Mai Shari'a na nan jihar Neja. Ta yadda ya zama tamkar wani abin bauta da ake tsoron saba masa a nan jihar. Kuma yakan yi abin da kawai ya ga shi ya dace masa ba tare da la'akari da wannan abin ya yi daidai da tsarin mulkin Nijeriya ko bai yi ba.

Duk da dai cewa ina rubuto maka wannan wasika ne bisa tunanin cewa, ku da ke can sama sam ba ku san abin da ke faruwa ba, don haka a tunanina za ku bincika ku tabbatar da matsayin halin da ake a ciki da nufin wanda nauyin gyaran lamarin ke wuyansa ya yi abin da ya dace.

A bisa wannan dalilin ne na rubuto wannan takarda domin a tabbatar da adalci ba tare da tunanin za a saba ma ko wanene ba.

Prince Ibrahim Dandodo Laka, ya aiko da wannan rubutun ne daga gida mai No.1 Awwal Ibrahim Road, Mypa Junction, Bosso jihar Neja





Komawa Shafin Farko