www.dillaliya.freeservers.com

DUNIYA LABARI:
Tare da Umar Abubakar 0802 363 9615

Abin mamaki! Aku ya fadi sunansa da adireshinsa

Helikwafta mai arhaWa ni tsuntsu (Aku) da ya yi kuskuren fita daga kejin da maigidansa yake ajiye da shi a wani gari mai suna Nagareyama, kusa Tokyo babban birnin kasar Japan, ya kuma yi batan kai. Sa’ilin da ya shiga watangaririya a cikin gari, ya shaida wa wani da ya tsince shi cikakken sunansa da kuma cikakken adireshin sa.

Da farko dai ’yan sanda ne suka ceto tsuntsun daga bisa wani rufin dakin tashar garin bayan jama’ar da ke wurin sun lura da cewa tsuntsun ya kwana, wanda abin ya ba su mamaki ganin ba saban ba, tsuntsu kamarsa ya kwana a irin wannan wuri. Ganin haka sai suka tsegunta wa ’yan sanda wadanda su kuma ba tare da wata-wata ba suka zo, inda suka sami nasarar kama shi da sauko shi daga wannan rufin. Jami’in ’yan sandan da ya jagoranci wannan aikin mai suna Shinjiro Uemura ya shaida wa manema labarai yadda tun da farko suka yi ta fama da shi wannan tsuntsun da nufin ko sa sami wani labari daga gare shi na ina ya fito, shi wanene ko kuma ina za shi? Amma tsuntsun ya ki ya ce masu uffan.

A bisa wannan dalili ne, in ji jami’in ’yan sandan ya zame masu tilas su maishe shi wani asibitin dabbobi na musamman, wanda a can din ne bayan wasu ’yan kwanaki kawai sai ya shiga hira da labarai tare da ma’aikatan da suke tare da shi. Inda bayan ya bayyana masu cikakken sunansa da lakabinsa, ya kuma bayyana masu sunan Maigidansa da sunan unguwarsu, kai har ma ya bayyana masu sunan layinsu da kuma lambar gidansu.

Ganin haka ya sa jami’an suka yi mamaki, nan ne kuma suka tambaye shi dalilin da ya sa tunda fari ya ki ya yi magana da su ko kuma ’yan sanda. Tsuntsun ya bayyana masu cewa ai shi tun farko bai gamsu da ’yan sandan bane, bai ga alamun jinkan halittu irinsa ba daga gare su, kuma ko da suka kawo shi nan asibitin, sai ya yi shawarar ya yi nazarin wurin da aka kawo shi da kuma yanayin wadanda suke tare da shi tukuna kafin ya ba da kansa. Ya ce gamsuwa da su da ya yi ne ya sa bayan ’yan kwanaki ya soma magana da su. A nan ne kuma ya rera masu wasu wakoki na yabonsu.

Jami’an suka ce bayan duk an gama wannan ne sai suka bi sawun adireshin da tsuntsun ya ba su, inda suka tarar da komai kamar yadda tsuntsun ya bayyana masu.

Ya ka gani, matukin jigin sama ya bugu da giya?

Wani matukin kamfanin jiragen saman Pinnacle Airlines Inc., da ya yada zango da nufin sauke wasu fasinjoji da kuma kara mai, ya yi tatil ya kuma yi marisa tare da wata mata mai aikin kula da fasinjoji a cikin jirgin nasa.

Matukin, mai suna Jeffrey Paul Bradford, dan shekara 24, da matar mai suna Adrianna Grace Connor, ita ma ’yar shekara 24 sun shiga wani wurin shakatawa ne da wasu ke gwangwajewa a daf da filin jirgin saman Harrisburg, inda su ma suka shiga dirkan maye, abin da ya saba wa dokar kamfanin jirgin saman na cewa ba za ka sha giya ba lokacin da kake shirin tuka jirgi.

Bayan dai sun yi tatil din ne sai suka yanke shawarar su shiga wani rukukin daji da ke nan kusa domin su yi lalata, kamar yadda mai raba barasa a wurin ya shaida wa manema labarai. Daga bisani ne dai sai da ’yan sanda suka zo da Helikwafta kafin a gano inda suka shiga, a sa’ilin da wsu makwabtan wurin suka tsegunta masu cewa sun hange su tsirara a cikin ciyayi. Haka kuwa aka yi, nan aka tsamo su tsirara a cikin ciyayin.

Sajan din ’yan sanda, Richard Brandt, ya ce tuni ma har an caje su da laifin rashin da’a, ganganci da kuma wasu laifukan. Amma ita kuwa matar an kara mata da tuhumar sata, saboda ita ce ta shiga wata karamar mota ta sato masu tocilar da suka yi amfani da ita wajen shiga jejin. Wani mai magana da yawun kamfanin Memphis, Tenn., Airline ya bayyana cewa tuni har an dakatar da wadannan tambadaddun daga aiki.

An daure wani mai kudi shekaru dubu

Wata kotu a kasar Masar ta daure wani hamshakin attajiri, kuma Biloniya mai suna Abdullah Kamel Muhammad har na tsawon shekara dubu a ranar Alhamis din makon jiya. An sami wannan fitaccen attajiri ne da laifin zambatan (419) mutane har 480. Kotun ta garin Giza can kasar Masar wacce take hukunta masu manyan laifuka, ta sami Abdullah Kamel Mohammed, mai kimanin shekaru 42, ne da laifin zambatan wadannan al’umma zunzurutun kudin da jimillarsu ya kai fam din Ingila har milyan 280, wanda jimlarsu ya kai Naira biliyan sittin har da hudu.

Mazambacin yakan shirya zambar tasa ce ta hanyar lallabar mutane da kuma janyo hankalinsu har su amince su ba shi kudaden nasu da sunan wai zai zuba masu su a cikin wata harka ta kasuwanci, wacce zai nuna masu yadda yin hakan zai kai su ga samun wata riba mai gwabin gaske. Ta haka ne dai ya yi ta yaudarar jama’a nan da can har na tsawon wasu shekaru, wanda da zaran kudaden sun shiga hannunsa shi kuma sai ya dafa layar zana.

Dubun Muhammad dai ta cika ne a cikin watan da ya gabata, inda ’yan sanda suka damke shi bayan da wani makwabcinsa da shim a ya taba fada wa komarsa, kwatsam sai Allah ya kwaranye masa hijabi ya gane shi. Tuni dai har ya fara zaman wa’adinsa na shekara dubu a gidan kaso.

Ta gutsire yatsan mijinta ta cinye

Wata mata a garin Hutchinson ta gutsire yatsan mijinta (Manuni) ta kuma cinye lakwam. Wannan mata mai suna Adelghun Khinde Johnson, mai kimanin shekaru 45 ta aikata wannan aika-aika ne bayan da wata ‘yar gardama ta hada su da maigidan nata a tsakar daren Asabar na makon jiya.

Jami’in ’yan sada Laftana Clay Rothe, ya ce bincike ya nuna masu cewa matar ta dunkule hannu ne ta daki mijin nata mai suna David Johnson har sau uku, wanda shi kuma mijin a sakamakon hakan ya sa hannu ya tunkude ta. Nan ne kuma ita matar ba tare da wani bata lokaci ba ta sami nasarar cafke yatsan mijin manuniya na hannun damarsa da hakoranta wanda ba ta saki ba sai da ta ji dirar yatsan a cikin tumbinta.

’Yan sanda sun ce matar ’yar asalin kasar Trinidad, tuni aka kama ta gami da dankwafar da ita a gaban kuliya, sai dai abin mamaki tun da sanyin safiyar Lahadi ne kotun ta ba da belinta a kan Dalar Amurka dubu biyar, ranar Juma’ar nan ne dai za a ci gaba da sauraron shari’ar.

Hanzarta ka mallaki naka!
Ga Helikwafta mafi kankanta kuma mafi arha

Kwanan nan ne za a kaddamar da wani sabon jirgin sama kirar Helikwafta a garin Vinci da ke kasar Italiya. Shi dai wannan jirgin, wanda a halin yanzun aka hakikance da cewa shi ne jirgin sama mafi kankanta, kuma mafi arha a duniyar nan, wani masani ne dan kasar Japan mai suna Gennai Yanagisawa, dan shekaru 75, ya kera shi. Jirgin saman yana iya daukar mutum guda ne kawai (wato mai abu da abinsa kadai), yana da nauyin kilogram 75 ne kawai. Kai za ka tuka abinka da kanka, babu ruwanka da iskancin direba. Jirgin kuma yana gudun kilomita 50 ne a sa’a daya.

Tuni dai har wasu mabukata sun biya kudin odarsu. Mutane biyar daga kasar Japan, biyu kuma daga kasar Amurka a kan kudin da ake sayar da shi, wato Dalar Amurka dubu hamsin da takwas da dari biyu da hamsin, wanda ya yi daidai da Naira milyan shida da dubu dari biyar. Wani mai sana’ar sayar da motoci a nan kasarmu da ya ji wannan albishir din cewa ya yi kwanan nan ne kasuwar motoci masu tsada za ta kau, domin kuwa shi ya tabbata masu kudin mu za su fi gwammacewa da su sayi wannan jirgin, tunda kudin sa ma bai kai na irin manyan motocin da suke saye suna shiga ba kamar su hummer jeep wacce kudinta sai ya saya maka wannan irin jirgin har guda biyar da ma canji.

Shi dai makirkirin wannan jirgin, Gennai Yanagisawa, ya ce yana son zuwa kasar Italiya ne domin ya kaddamar da wannan jirgi nasa a mahaifar Leonardo da Vinci, wanda aka hakkake cewa shi ne ya fara kawo fasahar jirgin sama na Helikwafta. Ya kara da cewa ya shiya hakan ne domin girmamawa ga wancan magabacin nasa, wato Leonardo da Vinci. “Ni ji na nake kamar almajirin Leonardo da Vinci, ina kuma fatan zuwan da zan yi takanas har can mahaifarsa in kaddamar da wannan jirgin zai faranta masa rai a can kabarinsa,” in ji makirkirin wannan jirgin.

Ya ma kara da cewa sai da ya je har can Vinci a watan biyu na wannan shekarar, inda ya kwaso tubarraki daga Sarkin garin a kan wannan aiki nasa. An dai sakawa wannan jirgin sunan GEN H-4, kuma a watan biyun ne dai na wannan shekarar shahararren littafin nan da yake kiyaye sabbin bajintoci na duniya wato “Guinness World Records” ya rattaba wannan jirgin saman a cikin shafukansa a matsayin jirgin da mutum kan iya shiga mafi kankanta a duniya.

Yanagisawa dai yana tafiyar da kamfaninsa ne na kera Helikwaftoci a garin Matsumoto da ke can Arewacin Tokyo. Shi da kansa ne kuma ya ce zai tuka wannan jirgin a can Vincin, inda yake sa ran watayawa da holewa a sararin samaniyar garin kafin a soma aikawa da masu kudi nasu.

Sun manta dansu jariri wajen rige-rigen shiga jirgi

Wasu iyaye da suka yi aniyar tafiya ta filin jirgin saman Westernmost da ke Canada, sun manta da dansu jariri mai kimanin watanni 23 da haihuwa a sa’ilin da suke hamzarin shiga jirgi ranar Litinin din nan da ta gabata.

Iyayen wannan jariri dai sun iso kenan daga kasar Philippines, to amma kokarin su kammala shirya kayayyakinsu masu yawa da suka taho da su daga can ya sa suka kusa kai su ga makarar kama jirgin da zai kai su inda suka yi niyyar zuwa, wato Winnipeg, don haka ne ko da isowarsu sai tilas ta sa suka rarrabu saboda sauri. Shi uban yaron mai suna Jun Parreno, ya zaci jaririn nasu yana hannun matarsa ne da surukarsa, wato mahaifiyar matar tasa, wadanda ya yi wa kokarin suka sami shigewa tunda fari.

Su kuma can sun dauka jaririn yana hannun uban ne, don haka suna nan tafe daga can baya. Kuma ko da duk suka sami sa’ar shiga cikin jirgin ba su sami kuma sa’ar zama wuri guda ba, a maimakon haka sai suka zauna wuri daban-daban, wanda wannan shi ya sanya ba su iya fahimtar cewa sun manto jaririn nasu ba can inda suka taso.

Bayan tafiyarsu ne dai jami’an tsaro suka tsinci yaron, wanda yake ta watangaririya a kofar shiga filin jirgin. Jami’an kamfanin jirgin saman kuma sun bayyana cewa ba su iya fahimtar cewa an bar wani a kasa bane saboda yaro ne karami wanda ba a bukatar a saya masa tikiti, sai dai kawai ya zauna a cinyar mahaifansa.

Jami’an tsaro dai na filin jirgin saman sun sami nasarar samun wani da yake jin yaren yaron na Tagalog, tunda yaron bai iya fahimtar harshen Turanci, wanda shi ne kuma ya yi ta kula da yaron har sa’ilin da mahaifin yaron ya sake yin wata tafiyar ta tsawon kilomita 2,300, daga can Winnipeg ya dawo Vancouver ya karbi yaronsa. Wannan dai shi ne karon iyayen yaron na farko da zuwansu Canada. Uban yaron kuma ya yi wa ma’aikatan kamfanin jirgin godiya kwarai da gaske saboda yadda ya dawo ya iske sun dukufa wajen kula da yaron nasa, wanda suka sayo kayayyakin wasa kala-kala suka jibge masa, shi kuma yana ta wasansa, awa bai iya fahimtar hatsarin da ya shiga ciki ba.





Komawa Shafin Farko