www.dillaliya.freeservers.com

Adamu Abubakar Babawo:
Dattijon da ya riki amanar Malam

Daga Ibrahim Muhammad

Sardaunan SakkwatoTun a baya can lokacin tsohuwar jihar Kano, kafin a yi jihar Jigawa, sunan Alhaji Adamu Abubakar Babawo ba boyayye bane. Kuma har yanzu amon sunan yana ci gaba da kadawa a tafarkin siyasar da ake aiwatarwa a kasar nan.

Tun daga soma siyasar wannan karni a 1999 har yau din nan, Babawo mutum ne da yake da tasiri a tafiyar siyasa, ba don komai ba, saboda dattijo ne mai ra’ayin fada da cikawa da kuma jan kowa a jika da tsayuwa a kan akidar siyasarsa.

Alhaji Adamu Abubakar Babawo, wanda yanzu haka shi ne mai bai wa Gwamna Malam Ibrahim Shekarau shawara a kan ayyuka na musamman, wato matsayin da a iya cewa ofishinsa na komai da ruwanka ne.

Shi ya sa ma a kodayaushe za ka tarar da ofishinsa cike da mutane kama daga ’yan siyasa mazansu da mata, matasa da sauran jama’a da suke zuwa da bukatu daban-daban da suke neman daukinsa a kai. Yana sauraron kowa da jawo ’yan siyasa a jika, wanda suke jam’iyya daya da ma wadanda suke da bambancin jam’iyya.

Don yana nuna masu mece ce siyasa, yaya ya kamata a tafi da ita, har hakan ta sa wasu barin jam’iyyunsu suka yi suka dawo cikin jam’yyar ANPP. Wannan irin hali nasa na kyautata wa ’yan siyasa tasa duk inda ka gan shi bai rabo da jama’a, gida ne ko ofis ko a tafe.

Dattijo ne da ake girmama matsayin siyasarsa da zamantakewarsa a duk fadin Kananan Hukumomi 44 na jihar. Yana tare da tasirin da dimbin jama’a suke tare da shi da goyon bayansa, wanda kyautata wa jama’a da yake yi ya zama sanadi. Yadda na fahimta, duk abin da ya mallaka ba ya kyashin mallaka shi ga ’yan siyasa, kullum hannunsa a bude yake wajen share hawayen ’yan jam’iyya daidai gwargwadon iyawarsa.

Yana daga cikin manyan wakilan Malam Ibrahim Shekarau da yawancin ’yan jam’iyya suke cewa sun fi aminci da shi, kuma yana daga cikin na sahun gaba a wajen kyautata wa ’ya’yan jam’iyyar ANPP, wanda dalilin haka ne ma tasa ake masa take da cewa, “wanda ya riki amanar Malam.”

Na taba jin wasu na cewa da ANPP a Kano na da mutane biyar masu hali irin na Babawo, da ’yan jam’iyyar ba su yi kuka ba, ko korafi a kan wasu ba su kulawa da su, duk kuwa da nauyin da Gwamna Malam Ibrahim Shekarau ya aza musu na amanar kula da jin dadin ’yan jam’iyya.

Za ka dada yarda da karamcin Babawo in ka je ka tarar da gungu-gungu na jama’a da yake sauraro ba tare da damuwa ba. Shimfidar fuska da yake musu, wannan wani hali ne na gogaggen dan siyasa da ya san martabar jama’a, yake kuma yin siyasa domin ya amfanar da jama’a.

Adamu Abubakar Babawo an haife shi a garin Barkeji a Azare. Kuma ya yi karatun ilimin addini a garuruwan Maiduguri, Azare da Kano. Tun yana harkar neman ilimi ya shiga siyasa a lokacin suna matasa, domin ra’ayinsu na son gaskiya da kuma kwato ’yancin talakawa da ake dannewa a wancan lokacin. Shi ya sa suka goyi bayan NEPU, suka yi ta, saboda a lokacin kusan duk bangaren masu neman karatun Kur’ani a wancan lokacin da aka fi kira da Gardawa, ita suke yi, su ake turawa su hana tauye hakkin talakawa in abin ya ci tura sai manyan ’yan NEPU su shigo.

Har a lokacin da aka kashe Firaministan Arewa, marigayi Ahmadu Bello Sardauna, Adamu Babawo suna karatu a Maiduguri, suna NEPU har aka shiga rigimar basasa aka gama. Dama Babawo tun tasowarsa mutum ne da yake shiga mu’amalar kungiyoyi masu zaman kansu iri daban-daban.

Da su aka kafa kungiyar kwallon kafa ta “Soccer Star” da ta yi tashe a baya can, ta kuma kyankyashe fitattun ’yan kwallo da suka yi fice da tashe a kasar nan. Yana kuma daga cikin ’yan kungiyar kwallon kafa ta kasa. Ko a lokacin da aka kafa PRP yana zuwa taronta da ba da gagarumar gudummawa amma bai taba sha’awar ya riki wani mukami ba sai da su Alhaji Ammani Inuwa suka takura masa sannan ya karbi mukamin Organizer na PRP, wanda a lokacin ana siyasa ta kishi ba domin abin da za a ba ka ba. Komai a lokacin, ’yan siyasa da kudinsu suke yi.

Ko lokacin siyasun baya, Babawo yana siyasa yana kuma dogara da sana’arsa ta tela. Ko lokacin da matsalar Abubakar Rimi da Malam Aminu Kano ta taso, Babawo ya bi bangaren tabo ne na Malam, saboda biyayya da tarbiyya ta siyasa da suka kwafa a wajensa. Har aka yi zaben da marigayi Sabo Bakin Zuwo ya ci Gwamna.

Bayan juyin-mulkin Buhari da aka dawo fafutukar kafa siyasa Babawo na daga cikin wadanda suka kafa wata kungiyar siyasa da take da rassa a duk fadin jihar Kano, wanda a sanadinta har aka kafa jam’iyyar NRC. Ba garin da Babawo bai je ba saboda kafa NRC, har sai da Kano ma ta zama cibiyar NRC, Alhaji Kabiru Gaya ya yi nasarar lashe zaben Gwamna.

Wannan ya nuna dama Allah ya yi wa Babawo baiwa na ya jagoranci ‘organization’ da cin zabe, domin kuwa ya kawo kujerar Kabiru Gaya a NRC a Kano. Kuma shi ne ya jagoranci samun nasarar da Alhaji Bashir Usman Tofa ya yi na tsai da shi takarar zama dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar NRC.

An tabbatar cewa duk lokacin da Babawo ya sa abu a gaba, sai ya kai ga nasara. An shaide shi mutum ne da kwadayi ba ya jan sa, mai ra’ayi ne da tirjiya a kan akida, kuma mai sassauci ne a kan maslahan da zai kawo ci gaba ga al’umma da kuma siyasarsa. Ba ya fifita kansa. Mutum ne mai saukin mu’amala, mai kuma tsananin zafi a lokacin da ka zo masa da abin da bai kamata ba, sannan yana da saurin sauka daga fushi.

Irin wannan halayya na jan ’yan jam’iyya a jika da karbuwa, meye sirrin haka? Babawo ya taba shaida min cewa abin da yake ba da nasara ga ’yan siyasa shi ne kyautatawa in kana da hali da rashin son kai. Don duk abin da ka fifita son kanka a kai sai dai ka yi baya.

Shi ya sa yanzu al’amura suka lalace na siyasa. Wasu na shigowa siyasa ne da hannun jari domin in an kafa Gwamnati a ba su mukami. Za ka ga ba ruwansu da ’yan jam’iyya da suka wahala wajen nema wa jam’iyya goyon bayan jama’a suka yi fadi-tashin kaiwa ga nasara.

Wanda ya sha wahala daban, wanda kuma zai zo ya ci moriya, ba ruwansa da ’yan jam’iyya kuma wannan shi zai ci gaba da haifar da matsaloli abin da zai kawo saukin haka ko waraka shi ne sai jama’a kowane bangare manya da yaransu sai sun gane cewa damokradiyya ba ta sayarwa bace, su san me ya kamata a ce sun yi domin ci gaban al’umma. Ko a baya can lokacin da Adamu Babawo ya fito takara ta neman shugabancin ANPP a jiha, wanda a lokacin masu zawarcin kujerar sun fito da yawa, kuma kowa yana ganin sai shi, amma Babawo ko da fitowarsa sai ’yan jam’iyya suka yi masa take da raba gardama, saboda sanin irin matsayinsa da tasirinsa a siyasa. Amma saboda maslahar jam’iyya da son ci gabanta da nuna Dattijantaka ya hakura ya janye, ya kuma mara baya aka yi zaben shugabancin jam’iyya cikin nasara.

Wannan mataki ya dada masa karamci da nuna wa ’yan jam’iyya irin tsananin kishinsa ga ci gaban jam’iyya, ta ajiye son ransa domin samun ci gaban jam’iyyar ANPP a Kano, musamman idan aka yi la’akari da irin dimbin nasarorin zaben da suka samu ba za su taba mantawa da irin dimbin rawar da Alhaji Adamu Abubakar Babawo ya taka wajen yakin neman zaben da ya kai ga nasarar kafa Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau a karon farko da na biyu a Kano ba.

A kodayaushe in ka gan shi ba shi da hutu wajen sauraron jama’a, musamman ’yan jam’iyya da sauran jama’a maza da mata. Masu neman tallafin karatu ne, makaranta ne, abin da za a yi sana’a ne. Babawo yana daga cikin ’yan jam’iyya da ’ya ’yanta suka shaide shi a kan yana rike da amanar kulawa da jam’iyyarsu da ’ya’yanta da Gwamna Malam Ibrahim Shekarau ya dora a kan hannun ire-irensa.





Komawa Shafin Farko