Yadda rayuwar Yahudawan Iran take
Daga www.dwelle.de/hausa
Duk da cewa Shugaban Iran, Mahmud Ahmedinejad na karyata aukuwar kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa a lokacin yakin duniya na biyu, wato Holocaust, to amma a kasarsa akwai gamayyar Yahudawa ta biyu mafi girma a yankin Gabas ta tsakiya baki daya.
Yahudawa a kasar ta Iran suna tafiyar da rayuwarsu ba da wata tsangwama ba, inda suke da ’yanci daidai da kowa. Suka ce suna tafiyar da addininsu da sauran al’adunsu ba da wata damuwa ba.
Alkalumma sun yi nuni da cewa akwai Yahudawa kimanin dubu 25 a Iran. Gabannin kaddamar da juyin-juya-halin Islam a shekara ta 1979 yawansu ya kai dubu 70. Daga cikinsu akwai Moses Saidan, wanda ya fi son a kira shi Baban Moses. Wannan mutumin mai shekaru 70 dan asalin yankin Isfahan ne da ke tsakiyar kasar Iran, kuma yana da kantinsa na sayar da kayayyakin tarihi da al´adu a layin Ferdausi da ke kusa da ofishin jakadancin Jamus da ke babban birnin Iran, wato Tehran.
“Ni Bayahude ne mazauni a birnin Tehran. Yanzu ana girmama mu kuma akwai zaman lafiya tsakaninmu da sauran al’ummomi. To, sai dai ba haka ya kasance ba bayan juyin-juya-halin Islam.”
Duk da cewa shugabannin addini a Iran ba su amince da wanzuwar kasar Isra´ila ba, sannan a kullum Shugaba Mahmud Ahmedinejad na nuna kyamarsa ga Isra´ila, amma Yahudawa na daga cikin tsirarun da ke da samun cikakkiyar kariya a jamhuriyar ta Islam.
Yahudawan Iran kamar sauran tsirarun addinai guda biyu, suna da wakilai a majalisar dokokin birnin Tehran. Baban Moses ya ce su fa Yahudawa ne, amma ba masu akidar kafa kasar Yahudawa ba. Dangane da abubuwan da suka shafi rayuwarsu a jamhuriyar ta Islam, Moses na mai ra´ayin cewa babu wata matsala duk da kalaman nuna kyamar Yahudawa da Shugaba Ahmedinejad ke yawaita yi.
“Muna da wuraren ibadar Yahudawa kimanin guda 20 a nan Iran. Kuma muna tafiyar da addininmu ba da wata tsangwama ba. A yankin Isfahan alal misali, muna da makabartarmu. Kuma a baya-bayan nan an gano wani dutse da ya kai shekaru dubu 3.
A matsayinsu na wata gamayyar addini, Yahudawa sun riga musulmi zuwa Iran fiye da shekaru dubu. Kasancewarsu a yankin ya samo asali ne tun bayan kame yankin Babylon a shekara ta 539 gabanin haihuwar Annabi Isa (AS). Yayin da wasu ’yan yankin Hebrew suka koma Palasdinu bayan an sake su daga kurkuku, wasunsu sun ci gaba da zama cikin wannan daula ta Babylon.
“Gaskiya mu a nan Iran ba mu da wata matsala da Yahudawa. Dole ne a ba wa tsiraru da ke cikinmu ´yancin rayuwa, kuma bai kamata a dame su. Kawo yanzu ban ji wani abu mai kama da tursasa musu ba.”
Lalle babu mamaki da Moses ke tattare da kwarin gwiwa. Domin yana da cikakkiyar masaniya kan yadda rayuwar yankin take. Yahudawan Iran dai na da wani matsayi na musamman, inda ake ba su izinin kai ziyara Isra´ila.
“Haka yake yanzu. Amma a shekaru takwas na farkon juyin-juya-hali ba a ba mu wannan izini ba. Yanzu kam ba da wata matsala ba muna iya zuwa Isra´ila mu kuma dawo. Hasali ma tsohon Shugaba Khatami na da kyakkyawar hulda da Yahudawa.”
To sai dai abin da Moses bai fada ba shi ne suna wannan tafiya ne ta wata kasa, musamman ta Turkiyya. A Iran dai ana bambamtawa tsakanin Yahudawa da kuma masu ra´ayin kafa kasar Isra´ila.
“A hakika kamar sauran ´yan Iran ni ma ba ni da wata matsala da Yahudawa. To amma dukkanmu muna da matsala da masu ra´ayin kafa kasar Yahudawa. Ai a cikin Alkur´ani ma an karfafa batun girmama Yahudawa da Kiristoci.”
Har yanzu ´yan Iran ba su da cikakkiyar masaniya game da kisan kare dangi da aka yiwa Yahudawa da ake yiwa lakabi da Holocaust. Saboda haka ne ma ba a wani nuna damuwa a cikin kasar ba lokaci da shugaba Ahmedinejad ya kwatanta kisan kare dangin da wata al´amara.
“Kisan kare dangin na Holocaust wani abu ne da ake yawaita yada jita-jitar sa. Ni ban yarda da aukuwarsa ba. Duk da cewa muna son Yahudawa a tsakaninmu, amma mun tsana kuma mun tir da kafa kasar Isra´ila da wadanda suka taimaka aka kafa ta.”
To sai dai tun a karshen shekarar da ta gabata abubuwa sun fara canzawa. Ganin yadda Iran ta yi kaurin suna wajen ba wa duniya mamaki, gidan telebijin kasar ya fara watsa wani jerin wasan kwaikwayo dangane da kisan na Holocaust, abin da ya janyo cece-kuce da suka daga wasu ´yan kasar.
Wasan mai rukunai 16 ya kunshi tarihin soyayya tsakanin wani dan Iran Habib Parsa wanda a lokacin da yake karatu a birnin Paris a cikin shekarun 1940 ya hadu da wata Bayahudiya ´yar Faransa da ake kira Sarah. Jim kadan sai sojojin Jamus suka mamaye babban birnin na Faransa kuma suka fara fatattakar Yahudawa. Parsa bai wata-wata ba sai ya fara tattaunawa da jami’an diflomasiyar Iran wadanda suka taimaka aka kwashe Sarah da iyalinta da sauran Yahudawa zuwa Tehran. Matasan Iran dai suna matukar sha´awar wasan kwaikwayon.
“Wannan shi ne karon farko da muka ga wani fim da ya nuna mawuyacin halin da Yahudawa suka shiga ciki. Fim din yana da ban sha´awa, musamman ga wadanda ba su da masaniya dangane da kisan kare dangi na Holocaust.”
Duk da cewa daukacin ´yan Iran ba sa kyamar Yahudawa kamar yadda furuce-furucen shugabansu ke yin nuni, amma nan gaba kadan yawan Yahudawa a Iran zai ragu, musamman saboda karuwar masu tsattsauran ra´ayin addini. To sai dai duk da haka in banda Isra´ila, Iran ta fi kowace kasa a yankin Gabas Ta Tsakiya yawan Yahudawa, inda suke zaman cude-ni-in-cude-ka da sauran mabiya addinai kamar musulmi da kiristoci.
Komawa Shafin Farko
|