www.dillaliya.freeservers.com

Dalilin da zai sa in daukaka kara
-Sani Sha’aban

Daga Abdullahi Tumburkai

Namadi Sambo,Wanda Shaaban ke karaKwanan baya ne kotun sauraron kararrakin zabe a garin Kaduna ta kori karar da Alhaji Sani Sha’aban, dan takarar Gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar ANPP. Kotun ta bayyana cewa ba ta ga wasu kwararan hujjoji ba da zai sanya ta soke zaben Gwamna Namadi Sambo. Don haka tsohon dan majalisar wakilai ta tarayyar ya bayyana cewa zai daukaka kara a hirar da ya yi da manema labarai.

TAMBAYA: Kotun sauraron kararrakin zabe ta Kaduna ta tabbatar da zaben Arch. Namadi Sambo na jam’iyyar PDP a matsayin Gwamnan jihar Kaduna. Me za ka ce game da wannan hukunci?

AMSA: Ra’ayina ba shi da bambanci da na masu tunani a kasar nan. Kowane mutum da ke jihar Kaduna ya san abin da ya faru, musammman lokaci zabe da kuma abin da ya biyo bayan zaben. Wannan abu ne da yake a bayyane, domin an gabatar da hujjoji tare da shaidu, takardu daga hukumar zabe (INEC) da dukkan takardun da ya kamata an gabatarwa da kotun. Sannan kuma ga kalubalantar tsayawata takara daga bangarori da dama, tsakanin ni ko Aruwa, har ya zuwa lakacin da kotu ta tabbatar da waye hakikanin dan takara.

Amma abin sha’awa shi ne, zan iya shaida wa ’yan Nijeriya da kuma jihar Kaduna cewa har yanzu muna da sauran dama. Muna sane da wannan hukunci tun kwanaki kadan kafin a yanke shari’ar. Wani babban mutum a kasar nan ya kira ni ya shaida min halin da ake ciki. Na yi bakin ciki, domin ni dan Nijeriya ne mai bin doka, don haka ko kwaro ba na son ya mutu saboda kawai Sani Sha’aban na son ya zama Gwamna. Don haka na yanke shawarar hada jakata don tafiya umura. Sai na tafi dakin Allah na zauna can na roki Allah Ubangiji.

TAMBAYA: Kana nufin ba za ka kalubalanci wannan Hukumci ba kenan?

AMSA: Takarduna na daukaka kara kashi 95 cikin dari sun kammala yanzu haka. Bisa ga al’ada ita wannan kotun da ta yi hukunci za ta ba da dukkan takardu na rubutu da kuma sauran shaidu da aka ba ta, idan muka hada wannan, to mun shirya. Na riga na fada wa Lauyana tun da mun ga ta inda suka bullo, to bai kamata ba mu zauna muna kallon su kawai ba. Na riga na bayyana cewa zan je kotun karshe a kasar nan don tabbatar da cewa al’ummar Kaduna sun sami ’yancinsu, bisa amanar da suka dora min na Gwamnan jihar na shekaru hudu. Ba wata barazana ko kuntatawa da za ta sanya in ja baya daga wannan matsayi.

Rayuwa daya ce, na rufe mahaifina, abokaina, abokan kasuwancina da kuma sauran mutane na kusa da ni da suka rasu. Don haka wane tabbaci nake da shi cewa zan kai anjima? Duk abin da nake yi ina yin sa ne da niyyar cewa ba zan kai minti daya da rai ba. Wannan shi ne tunanina, don haka zan daukaka kara. Za mu ci gaba har sai mun kai kololuwa. Idan akwai bukatar zuwa kotun koli, to za mu je can. Muna da hujjojin da suka tabbatar da cewa mu muka lashe zabe. Har wadanda suke kan mulkin sun san haka. Kuma za a iya ganin tsare-tsaren Gwamnati na cikin mawuyacin hali. Saboda yanzu suka farka, kuma ba su yi tunanin haka ba. Sun dauke su ne kuma suka watsar da su, sannan kuma su ce da kai ga abin da za ka yi. Wannan ne abin da al’ummar Kaduna ke fama da shi. Amma mun san addu’armu ba za ta tafi kawai ba.

TAMBAYA: Me wannan babban mutum ya shaida maka?

AMSA: A yanzu, tunda na yanke shawarar daukaka kara, to mun riga mun manta da wancan, saboda ba Sani Sha’aban aka cuta ba, kuma ba wai kawai mutanen jihar Kaduna aka zalunta ba. Tsarin ne gaba daya ake son batawa. Wannan tafiya ba wai ana yin ta bane don Sani Sha’aban ya zama Gwamna. A’a, ana yin ta ne don ganin mulkin dimokradiyya na gaskiya ya tabbata a Nijeriya. Ba wai dimokradiyyar gado ba, wadda da zarar wa’adin mulkinka ya kare, sai ka nemi wani na kusa da kai, dan uwanka ko abokinka, ka ce da shi ya zo ya ci gaba. Wannan ba dimokradiyya bace sam.

Kamata ya yi a yi mulkin dimokradiyya Nijeriya kamar yadda take a sauran kasashen duniya. Kuma na tabbata idan mutane suna jin tsoron Allah, sannan sun san abin da Kur’ani da Baibul suka kunsa, tabbas ba za su kasance kan kujerar da suka san cewa ba su cancance ta ba. Ba za ka iya amfani da dukiyar jama’a ba, ba tare da ikonsu ba. Tambaya nan ita ce shin al’ummar Kaduna na jin dadin wannan abu kuwa? Ba wai kawai kwasar kudinsu a kai ajiya kasashen waje ba. Lallai ba irin wannan gwamnati al’ummar jihar Kaduna ke so ba.

Idan ka zagaya Kananan Hukumomi da kuma kauyuka, idan ka ga yadda ake fama da talauci, abin zai ba ka tausaye. Tafi makarantun jihar Kaduna ka gani. Sai ka zubar da hawaye. Za ka ga matashi cikakke wanda ya jima da kammala karatu yana garari a layi saboda ba shi da aikin yi. Wannan ba ya faruwa? Jihar Kaduna jiha ce mai arziki. Da kudaden Tarayya ko babu zan iya mulkin jihar Kaduna. Ina tabbatar maka da haka. Mun san noma yadda ya kamata, sannan kuma ga mu da kasar noma isasshiya, sannan kuma al’ummarmu ba ragwaye ne ba.

TAMBAYA: Bisa wace hujja za ka kalubalanci wannan hukunci?

AMSA: Abu mai saukI ne kuma a bayyane. Mun shiga zabe, kuma dukkan sakamakon zaben da muka kai wa wannan kotu, mun nemi Alkalan da su duba da idon basira. Dukkan wadannan hujjoji ba Sani Sha’aban ne ya buga su ba. Sune ainihin sakamakon zabe da INEC ta yi daya bayan daya. Muna da dokar zabe wadda ta bayyana yadda za a gudanar da zabe filla-filla da kuma wadanda ya kamata su tsaya a wannan zaben. Saboda haka a bayyane yake cewa an saba wannan dokar zabe din ta hanyar yin abubuwan da ba daidai ba a zaben. Don haka idan muna bin doka da oda, to wajibi ne mu bi tsarin mulki kamar yadda dokokin zabe suke.

Takardun da muka mika wa kotu hujjoji ne sahihai, sannan ina kalubalantar kowa cewa ya tafi inda Namadi Sambo yake ya bincika, cewa (Namadi) ya ci zabe a unguwarsa? Idan ina son in san kai ko wanene, zan fara ne daga makwabcinka. Idan makwabcinka ya ce kai ba ka cancanci ka jagoranci al’umma ba, to kai har waye da za ka fito ka bayyana kanka? Wadannan abubuwa ba a boye suke ba. Ba ni da sabani da Namadi. Abin da kawai ya dame ni shi ne wannan tsari. Ba ni da lokacin

sabawa da wani. Allah (SWA) ya yi mani budi ta hanyar kasuwancina sama da shekaru 17 zuwa 18. Don haka ina wa Allah godiya, kuma ina iya cewa kamfanina na safarar jirgin ruwa na tafiya yadda ya kamata. Ba zan iya bayyana yawan ma’aikatan da ke aiki a karkashina ba.

Ba za mu iya cewa mu musulmai ko kiristoci na gari bane, alhali muna kan abin da muka san cewa ba hakkinmu bane, ba mu cancance shi ba, ba mu same shi ba. Idan muka yi haka, ta yaya za mu iya yi wa wasu fada?

TAMBAYA: Bisa abin da ya faru da kararka, me za ka ce yanzu, har yanzu kana kallon bangaren shari’a a matsayin dama ta karshe ga talaka?

AMSA: Kada ka manta da abin da na ce game da wannan hukuncin. Tabbas bangaren shari’a sun faro aiki mai kyau, don har kungiyoyin kasashen waje sun yaba masu, to amma abin takaici muna tunanin wannan abu zai dore, amma ina!

Abin shi ne mutane masu hali mai kyau da kuma fata ta gari sun koma gefe. Idan kana da tsari mai kyau, amma ba ka da kudi, ba za ka bata lokacinka ba. Idan kana da kudi, amma ba ka da tabbacin kana cikin kungiya mai karfi, to ba za ka yi tunanin shiga ba. Saboda haka za mu ci gaba kenan da samun abin da ake kira da Ubangidan siyasa da yaronsa. Wanda zai ce “kai yarona ne zo ka karbi mulki.” Ina wannan abu zai kai kasar nan Nijeriya?

Idan ka kalli Nijeriya har ma ta bangaren wasanni da kuma wasu bangarorin muna wata irin tafiya ne. Mun dan tsaya kadan a Adis Ababa (kasar Ethiopia) yau. A ’yan awannin da muka yi ba a dauke wuta ba ko kadan. Ko ka san abin da kasar ta dogara da shi wajen samun kudin shiga, to kofi ne (coffee). Shin mutum nawa ne suke shan kofi? Abin da kawai suke da shi kenan, amma suna alfahari. Yanzu haka Ethiopia su ke da jirgin sama na zirga-zirga mafi nasara a Afirka. Shin wannan ba abin kunya bane gare mu?

A Nijeriya, ka san cewa ban cancanta ba, amma sai ka ce in yi, tafi majalisar wakilai. Ba ka san aikin dan majalisa ba, amma an tura ka can. Abin da kawai ke gare ka shi ne abin da zai shigo aljihunka. Haka ma a majalisar Dattawa, Gwamnoni da ma shugaban kasa da sauran mukamai. A karshe kafin a farga tsarin ya ruguje. To, wannan abin muke gudun faruwarsa. Ba wai muna son sai Buhari ya zama Shugaban kasa bane ko Sani Sha’aban ya zama Gwamna. A’a, wannan tsarin ne muke son ganin bai fadi ba. Wannan kamar wata gwagwarmaya ce a boye muke shirin yi.

TAMBAYA: Kana shirin zuwa kotun daukaka kara, to menene sakonka ga magoya bayanka?

AMSA: Da farko ina godiya ga Allah Madaukakin Sarki. Sani Sha’aban ba kowa bane. Wasu sun manta cewa Sani Sha’aban bai taba neman ya zama Gwamna ba. Jama’a ne kawai suka yi ta goyon bayana ta kowace fuska. Lokacin yakin neman zabe na shiga lungu da sako na jihar Kaduna tare da motoci sama da dari uku. Wani lokacin mu kwana a kan titin kauyuka. Ina tabbar maka da cewa kafin mu shiga gari da kolimita biyar ko bakwai za mu tarar da matasa da dattawa da kuma mata sun zo tarbar mu. Saboda haka mutanen jihar Kaduna sun nuna mani kauna. Sannan ina tabbatar masu da cewa in har muna raye ina addu’ar Allah ya ba ni damar da zan tabbatar masu da kaunar da suka nuna mani cewa sun yi dan halas, ba zan bar su su yi da na sani ba. Saboda haka mutane su kwantar da hankalinsu. Za mu ci gaba da addu’a ga Allah Madaukakin Sarki tare kuma da bin hanyar da ta dace, ba tashin hankali ba don karbar hakkin talakawan jihar Kaduna.



Komawa Shafin Farko