JAWABIN DAVID UMARU GA ’YAN JARIDA
Ya ku ’yan jarida
Ina matukar jinjina maku bisa dauriyarku a kan hakan. Wannan duk a bisa kyakkyawar fatanmu ne na cewa ba mu fid da kauna ba, muna nan kuma tsaye kyam tare da tabbacin sai mun kwato kujerar nan da kuka ba mu wacce barayi suka sace.
Tun bayan wancan zaman da muka yi da ku, abubuwa masu daman gaske sun faru a wannan jiha tamu ta Neja, wadanda ba shi yiwuwa mu runtse idanunmu ko mu yi gum a kansu, saboda yadda suka kasance sun shafi rayuwar al’ummarmu. Don haka ya zama tilas mu yi magana a kansu. In kuwa har muka yi shiru, to mun tabbata tarihi ma ba zai yafe mana ba.
A ranar 29 ga watan Maris ne gwamnatin Dakta Mu’azu Babangida Aliyu, ta hanyar amfani da wata kafa nata wacce ake kira wai Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Neja ta gabatar da wani abu wanda tarihin wannan jiha tamu ba zai taba mantawa da shi ba a matsayin wani lokacin da aka yi wa tsarin dimokradiyya karan tsaye aka kuma tozarta tsari da kuma dokokin zabe, babu kunya babu kuma tsoron Allah da sunan wai zaben Kananan Hukumomi.
A karshen wannan aiki da aka yi na wasa da kwakwalan jama’a da sunan zabe, sai ga shi babu ko kunya bare fargaba na irin ta’asar da ta aikata ita wannan ’yar kore mai suna Hukumar zabe mai zaman kanta ta jiha, ta fito fili ta bayyana jam’iyyar PDP da cewa wai ta cinye zaben kujerar shugabannin Kananan Hukumomi guda 25 da muke da su a wannan jiha tamu, kuma ma baki dayan kujerun Kansilolin da muke da su idan ka debe guda 8, to su ma wai duk PDP din ne wai ta cinye su.
Ya ku ’yan jarida, na tabbata kuna nan a ranar da aka ce wai an yi wannan zaben, na kuma tabbata sai dai in ku ma kun zabi danninya da rashin adalci ta hanyar yin gum da bakinku, amma na tabbata ba tare da wani juyayi ba za ku yarda da cewa abin da aka yi a ranar 29 ga watan Maris a nan jihar Neja sam bai yi kama da zabe ba. An dai yi sata, an yi murdiya, an yi magudi, an murkushe wa jama’ar jiharmu damarsu da suka dora wa wadanda suke ganin amintattu ne, sun kuma yarda da su, da su damka masu amanarsu a mataki na Kananan Hukumomi.
Ayyukan magudi iri-iri ne suka cika wannan zaben, rikice-rikice da ta da yamutsi da gangan irin na ’yan iska da aka turo kuma aka biya su ne suka faru a ko’ina cikin fadin jiharmu a wannan ranar. Ko ina ka duba ’yan bangar siyasa ne da ’yan daba masu alfaharin suna yi wa gwamnatin jiha aiki ne dauke da kowane irin nau’in makami suke cin karensu babu babbaka, suna tsoratarwa gami da cin mutuncin bayin Allah na gari da suka fito su kada kuri’unsu a wannan ranar. Irin wadannan ’yan banga da ’yan daba haka suka rika bin tashoshin zabe suna kwatar akwatunan kada kuri’u, wasu wuraren su fasa,wasu wuraren kuma da ba su samu damar kwacewar ba su sa hannu a aljihunansu su dumbuzo takardun kuri’un da suka rigaya suka daddangwale su, sannan su sa karfin tsiya su danna su a cikin wadannan akwatuna, da fa rana kiri-kiri. Kawai wai su suna takamar wai gwamnati tasu ce, a cewarsu. Haba jama’a! Wannan har ina? Da haka ne da wadannan ’yan iska suka ci gaba da tsoratarwa gami da cin mutuncin jama’ar da ba su ji ba ba su gani ba, kawai don suna alfahari da gwamnati suke wa aiki. A wasu wuraren sun raunata jama’a masu dama, kama daga jami’an tsaro masu kula da aikin zaben da su kansu ma’aikatan zaben gami da ’yan jarida masu aikin sa ido da dai sauran jama’a masu yawa. Wurare da yawa sai da ta kai ga an kwantar da wasu a asibitoci.
Ya ku jama’a, na tabbata wannan ba zai ba ku wani mamaki ba idan da har kun san cewa duk wannan ta’asar da gwamnatin PDP da ’yan bangarta suka tafka wani shiryayyen abu ne wanda aka dade da shirya shi kwanaki da yawa ma kafin zaben. Idan har za ku iya tunawa da yadda tun ma kafin gudanar da wannan abin da aka kira da sunan zabe, Mu’azu Babangida Aliyu ya yi ta babatun cewa lailai ko ana ha-maza-ha-mata ko jama’ar jihar Neja sun zabi PDP, ko ma ba su zabe ta ba, PDP din ce za ta lashe daukacin kujerin Kananan Hukumomi 25 da muke da su a wannan jiha gami da na Kansiloli baki daya. Ya yi wannan magana wacce kuma ya rika nanatawa a wurare masu yawa. Ya yi wannan magana a nan garin Munna, ya fada a Suleja, ya sake nanata ta a Kwantagora, ko zuwansa Bidda ma ya sake nanata wannan maganar.
Idan ma ba ku manta ba irin wannan munanan kalaman nasa ne ma na takala ya janyo mummunan rikicin da aka yi a garin Suleja, a kuma kofar fadan Sarkin na Suleja ranar Juma’ar 21 ga watan Maris. Wanda kuma a sakamakon wannan yamutsi da ’yan bangar da daman Mu’azu Babangida Aliyu da abinsa ya tafi can suka haddasa wa jama’armu da babu abin da ya hada su da wannan gangami nasa ne suka jikkata babu gaira babu sabar. Wanda a karshe har suka gama tsiyatakunsu da iface-ifacensu ko da mutum guda daga cikinsu ba a kama ba. Sai ga shi ko kunya babu an bi magoya bayanmu da babu ruwansu ana ta kamawa ana tsarewa, wanda kuma haka aka ci gaba da tsare su har sai da aka gama zaben ne sannan aka fiddo su.
Wata dubarar rashin dubarar kuma da suka yi amfani da ita shi ne inda suka rubuta wasu jerin sunaye masu yawa na wadanda suka tabbatar magoya bayanmu ne suka bai wa jami’an hukumar ’yan sanda da sunan wai ana zargin sune masu haddasa fitina. Suka kuma yi umurnin da a kama su a tsare, wai har sai an gama zaben. Ni a Karamar Hukumar da na fito (Wato Karamar Hukumar Shiroro) sunayen mutane 25 ne aka mika wa jami’in ’yan sandan Erana domin ya kama su. Cikin su kuwa har da Shugaban mazabata. Sun kuma sami sa’ar kama mutane 9 daga cikinsu, suka kuma damka su ga babban Shugaban ’yan sandan yanki, DPO a can Shiroro. Sai bayan da jama’an yankin suka nuna rashin amincewarsu ne, inda har sai da suka kai kukansu ga Kwamishinan ’yan sanda ne sannan da kyar suka yi nasara aka sake su.
Kuma ba su gudanar da wannan zaben ba sai da suka tabbatar da cewa duk wani jami’i, kama daga masu lura da akwatuna zuwa masu duba su, da dai duk wani mai aikin zaben nan, imma dai daman dan jam’iyyarsu ne ta PDP, mai cikakkiyar rajista ko kuma wani dan uwa ne na kut da kut ga dan takarar da ke wannan mazabar. To, duk a cikin wannan dambarwar nasu abin da ya fi bai wa kowa mamaki ma shi ne na wata takarda da ta fito daga Hukumar zabe mai zaman kanta ta jiha, inda take bayyana cewa wai ba za ta yarda ’yan takararmu su tsaya a zaben ba, wai a cewarsu tunda wasu daga cikin tsaffin ’yan jamm’iyyarmu da aka kora can baya sun shigar da kara a kotu suna kalubalantar korar su da aka yi. Wannan abu ya bai wa kowa mamaki, domin idan ma har hakan ne, to me ya hada wata matsala tamu ta cikin gida da abin da ya shafi shigar mu zabe?
Muna kuma sane da barazanar da aka yi wa jami’an gwamnati, masu unguwanni, dagatai da sauran masu rike da sarautun gargajiya na cewa matsawar PDP ta fadi a yankunansu, to kuwa a bakin aikinsu ne ko kuma rawunansu. A yanzun haka ma akwai sunayen da aka rattaba domin dakatarwa ko kuma sallama baki daya na wadanda ake zargi da cewa basu tabuka wa PDP komai ba a yankunansu.
Ya ku ‘yan jarida, daga cikin abin kunyan da ya faru na irin magudin zaben da suka shirya shi ne. Kwanan Mariga, inda jami’an tsaro suka harbe wani dan bangar PDP, wanda ya yi kokarin satar akwatin zabe, jama’ar wurin kuma suka tirje. Yanzun haka wannan maganar tana hannun ’yan sanda. Na kuma tabbata kun ma fi ni cikakkiyar masaniya a kansa. A Karamar Hukumar Shiroro, wanda kowa ya san wani yanki ne da ANPP take da rinjaye mai karfi sosai, aka turo ’yan daba suna kwace akwatunan zabe da karfin tsiya. A wasu mazabun ma jami’an tsaro ma da kansu aka samu suna wannan aika-aikar. A wasu mazabun ma da yawa kamar a Allawa da Manta, wakilan ANPP, an ci mutuncinsu matuka, kuma kayayyakin zaben ma ba su isa ga mazabu ba inda ma suka isan, to kuwa sai da aka tabbatar da cewa ’yan kwaranni ne kawai aka kai masu da ko kusa ba za su wadatar da masu zaben ba. A mazabata a Kaure Kwaci/Kuciba akalla dai mazabu 12 duk ba a yi zaben ba, amma an bayar da sakamakon zabe. A mazabar Gussoro da Zumba an gudanar da zabe kuma an bayar da sakamakon zaben tun a nan tashoshin zaben, amma sai ga shi daga baya an ce wai an soke wannan zaben ba tare da wani dalili ba. Kawai wai saboda ANPP ce ta cinye zaben. Haka nan a Munya da sauran wasu Kananan Hukumomin inda sam ba a gudanar da zaben ba, amma kuma aka bayyana jam’iyyar PDP, da cewa wai ta cinye zabe.
To, ko ma dai menene, ya ku jama’ar jihar Neja na tabbata babu wani mai hankali da duk son lullube gaskiyarsa zai yi tunanin cewa wai an gudanar da wani zaben Kananan Hukumomi bisa gaskiya da adalci ba tare da magudi ba a nan jihar Neja. Zabe ne da ya kamata ya zama abin takaici da kunya ga duk wani mai hankali dan jihar nan tamu ta Neja da ma kasarmu baki daya.
Har ma wai muhawara wasu ke yi wai wannan nasarar da suke riyawar sun samu ta samu ne saboda ayyukan raya kasa da gwamnatin Dakta Mu’azu Babangida Aliyu ta aiwatar daga lokacin da ta hau karagar mulki. Wannan abin dariya ne, domin kuwa ni da ku duk mun san da cewan tun daga lokacin da Mu’azu Babangida Aliyu ya hau karagar mulki, kullum haka nan yake ta babatun gudanar da muhimman ayyuka daban–daban, amma har ya zuwa yau din nan ko da guda daya ba mu ji ko a labarai an ce za a kaddamar da shi ba, ko da kuwa da ba’a ne ma, wai an ce wa kare ana buki a gidanku ya ce mu gani a kas.
Matsa Nan
|