www.dillaliya.freeservers.com

Gwamnatin Shema ba ta tsinana wa Katsinawa komai ba
In ji Sanata Abu Ibrahim

Daga Abdullahi Tumburkai

ta a kan al’ummar jihar na dab da cika shekara guda, amma har yanzu ba a ga inda ta dosa ba game da tallafa wa al’ummar wannan jiha da ke fama da talauci.

Abu Ibrahim ya bayyana makudan kudin da aka ce jihar na ajiye da su da cewa badi ba rai ne domin a al’ummar jihar na fama da talauci, amma Gwamnatin jihar ta gaza fito da wata hanya da za ta iya rage wa jama’a halin da suke ciki.

Tuni dai Gwamnatin jihar ke babatun cewa tana ajiye da sama da Naira miliyan dubu talatin da biyar a asusunta. Don haka, Abu Ibrahim ya kara da cewa Kananan Hukumomin jihar suna nan cikin wani hali saboda har zuwa yanzu ba su iya aiwatar da komai a Kananan Hukumominsu.

Gwamnan jihar kuma har yanzu yana ci gaba da nuna halin ko-in-kula, dangane da inda jihar ta sa gaba, ballantana har ya fuskanci matsalolin da al’umma ke fama da su ta kowane bangare.”

Wani abu da Sanatan ya bayyana shi ne, Gwamnan jihar ne ya fi kowane Gwamna yawo a kasar nan, domin, a cewarsa, tunda Gwamnan ya hau kujerar mulkin jihar zai wahala idan ya taba yin mako biyu a jihar ba tare da ya fita ba.

Ya kara da cewa al’ummomi da yawa na fama da rashin ruwan sha, sannan mutane da yawa na mutuwa saboda cututtukan da suke fama da su saboda rashin kulawar Gwamnati ga asibitoci, kana kuma talauci da rashin tsarin ma’aikata na kara kashe darajar aikin Gwamnati a jihar.

Ya ce, ma’aikatan jihar a irin wannan hali suka gudanar da bukin ranar ma’aikata ta bana ba tare da an biya masu bukatunsu ba da aka yi masu alkawura.





Komawa Shafin Farko