www.dillaliya.freeservers.com

Magoya bayan Shinkafi da Yarima sun gwabza a Gusau

Daga Shu’aibu Ibrahim Samaru

Ganau sun shaidawa DILLALIYA cewa wasu matasa da ke bayyana cewa su magoya bayan Gwamnan jihar ne suka dirarwa ofishin magoya bayan tsohon Gwamnan da ake kira da ‘Yarima Solidarity Association’, inda suka yi kaca-kaca da ofoshin tare da lalata hotunan shugaban kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa da kuma na tsohon Gwamnan ke cikin ofishin, tare kuma da yin amfani da bakin fenti don lalata farin bangon ofishin wanda bene ne hawa daya.

Wasu mutane shida da suka yi kokarin hana abin da matasan ke yi sun sha dan karen duka kafin a turo ’yan sanda wurin don dawo da doka da oda.

Wannan abu dai ya faru ne yayin da Gwamnan jihar ba ya kasar, domin ya yi balaguro zuwa kasashen waje a tafiyar da za ta dauke shi makonni uku.

Da yake tsokaci kan abin da ya auku a ofishinsa, Kwamishinan watsa labarai na jihar, Alhaji Ibrahim Danmalikin gidan Goga ya zargi tsohon Gwamna Alhaji Ahmad Sani Yarima da yunkurin ruguza abin da Gwamnatin ke yi. Ya ce yanzu an riga an shata fage tsakanin Yarima da Shinkafi. Don haka ya ce ba za su bari a ruguza masu Gwamnatinsu ba, za su yi duk yadda za su yi don ganin sun kare ta.

Wata majiya ta shaida mana cewa wannan rikici ya samo asali ne bayan da jam’iyyar ANPP mai mulki ta rubuta wa Kwamishinan ’yan sanda na jihar, inda ta bayyana cewa ta haramta duk wani nau’in taro na siyasa a dukkan fadin jihar.

Takardar, wadda mataimakin Sakataren jam’iyyar ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa ba wani dan jam’iyyar da ke da hakkin manna fostarsa ko kuma bude ofis a dukkan fadin jihar har sai da izinin Gwamnan jihar a rubuce.

Jam’iyyar ta kara da cewa ta kuma hana duk wani nau’in taro da kuma tarbar wani dan jam’iyyar a jihar har sai da izinin Shugaban jam’iyyar a rubuce. Takardar mai dauke da kwanan wata 5 ga Mayu, an mika wa rundunar ’yan sanda ita ce kwana guda kafin magoya bayan Yarima su bude wannan ofishi a Gusau.

Kwamishinan ’yan sanda na jihar Muhammad J. Abubakar, ya tabbatar da karbar wannan takarda. Ya ce kuma ya shawarci shugabannin ‘Yarima Solidarity Association’ da su nemi izinin Gwamnatin jihar don samun zama lafiya.

“Game da izinin yin taro ko rali a wannan jiha na shaida wa jam’iyyar cewa wannan dama ce ta rundunar ’yan sanda. Ba wani ko wata jam’iyya da ke da damar bai wa wani ko wasu damar yin taro a wannan jiha sai rundunar ’yan sanda. Ban je wannan ofishi ba, amma na sami labarin cewa hoton Shugaban kasa ne a wurin. Kuma aikina ne kare hoton Shugaban kasa. Don haka tuni na tura ’yan sanda don kare hoton Shugaban kasa,” in ji Kwamishinan.

Wadannan matasa da suka je wannan ofishi sun ci karfin ’yan sanda da aka tura, inda suka yi raga-raga da hoton Shugaban kasar tare kuma da raunata wasu mutane shida da ke ofishin.

Jim kadan da yin wannan abu, wasu matasan da suka kira kansu magoya bayan Yarima suka bazama kan titi runa rera wakokin Allah wadai da Gwamna Shinkafi, tare kuma da bayyana cewa suna fama da yunwa, rashin aikin yi da kuma rashin ruwan sha mai kyau.

Kwamishina Abubakar ya bayyan cewa mutanensa sun tarwatsa masu zanga-zangar, amma ba su kama kowa ba, saboda a cewarsa matasan ba su yi wa ’yan sanda wata barazana ba. Ya kuma tabbatar da cewa rundunarsa na nan na binciken musabbabin wannan abu.

Yaunkurin jin ta bakin Sanata Yarima ya ci tura domin masu tsaron gidansa sun bayyana cewa ya koma Abuja, amma wani na kusa da shi wanda ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa Yarima ya sha bayyana cewa kada wanda ya ta da rigima saboda shi.

“Ya kira ni a waya, ya shaida min cewa in fada wa magoya bayansa cewa kada wanda ya yi fada saboda shi. Har yanzu a wurinsa mu duk ’yan jam’iyyar ANPP ne saboda haka ya ce bai dace ba mu yi fada bisa ko wane irin dalili ne. Ya kuma ce in sanar da mutane cewa ba shi da matsala da Gwamna Mamuda Shinkafi. Duk abin da faru mutane su yi sulhu shi ya fi,” in ji shi.





Komawa Shafin Farko