www.dillaliya.freeservers.com

Sake Zaben Gwamnan a Sakkwato:

Ba mu amince da zaben ba - DPP

Zabe ya yi kyau – INEC
A zo a hada kai - Wamakko

Daga Abdullahi Tumburkai

Wamako Wannan zabe dai kotun daukaka kara ta Kaduna ce ta ba da umurnin a sake shi bayan ta soke zaben da aka yi wa Gwamna Alu Magatakarda Wamakko bisa rashin bin ka’ida da aka yi wajen tsayar da shi takara tare da mataimakinsa Alhaji Muntari Shehu Shagari.

Dan takarar Gwamna na jam’iyyar ta DPP Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi ne ya bayyana haka jim kadan da bayyana sakamakon zaben da Hukumar zabe ta kasa ta yi ta hannun Kwamishinan zabe na jihar, Alhaji Hasan Yahaya.

Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi ya bayyana cewa ba wani zabe da Hukumar zabe ta kasa za ta shirya a ce an yi shi bisa ka’ida. Ya kuma ce jami’an tsaro sun musguna wa Wakilansu na rumfunan zabe tare kuma da takura wa dukkan magoya bayan jam’iyyarsu.

Don haka ya ce jam’iyyarsu ba ta sanya hannu a wannan sakamako ba, wanda ya ce da sun yi hakan, to da sun amince da zaben kenan. Ya kara da cewa dama suna kotu inda suke kalubalantar tsayawar Alhaji Alu Magatakarda Wamakko wannan zabe. Ya ce ba gudu ba ja da baya a wannan shari’a da suke yi har sai sun kwato wa al’ummar jihar Sakkwato hakkinsu da aka kwace musu.

Ya bayyana saurin bayyana wannan sakamakon zabe da Hukumar zabe ta yi ya nuna cewa akwai wani abu da aka shirya, domin a cewarsa, a tarihin jihar ba a taba bayyana sakamakon zabe kasa da awanni 48 da kammala zabe ba. Amma wannan zabe an bayyana sakamakonsa ne da asubahin ranar Lahadi. Daga nan ya tamabaya, me ya sa wannan zabe ya fita da ban da sauran zabubbukan da aka saba yi a jihar? Sai ya yi kira ga sauran magoya bayansa da su kwantar da hankulansu su zauna lafiya su jira su ga abin da kotu za ta yi.

Shi kuwa zababben Gwamna Alhaji Alu Magatakarda Wamakko, godiya ya yi ga magoya bayansa bisa namijin kokarin da suka yi har suka ga ya kai ga nasarar lashe wannan zabe.

Daga nan ya yi kira ga wadanda ba su sami nasara ba da su dau hakuri da kaddara su zo don a taru a ciyar da jihar ta Sakkwato gaba. Ya ce, dukkan wadanda suka fito wannan takara suna son ci gaban jihar Sakkwato ne, don haka bai ga dalilin da za su juya baya su yi adawa ba.

Hadaddiyar kungiyar ’yan takarar Gwamna na jam’iyyun siyasu ta jihar ta taya zababben Gwamna murnar wannan nasara da ya samu. A taron da ta kira da maraicen ranar Lahadi, Shugaban kungiyar kuma dan takarar Gwamna na jam’iyyar adawa ta ADC, Alhaji Malami S. Galama, ya bayyana wannan zabe da cewa zabe ne da aka yi shi bisa gaskiya. Sannan ya yi kira jama’ar jihar Sakkwato da su goya wa wannan Gwamnati na Wamakko baya.

Taron, wanda ya sami halartar kusan dukkan ’yan takarar da ba su yi nasara ba illa kawai na DPP da bai zo wannan taro ba, sun jinjina wa Hukumar zabe ta kasa da kuma jami’an tsaro bisa kokarin da suka yi aka kammala wannan zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Ita kuma hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana zaben na Sakkwato da cewa shi ne mafi kwanciyar hankali da Hukumar ta yi a cikin zabubbukan da aka sake bisa umurnin kotuna. Ta ce al’ummar jigar sun nun halin dattaku a wannan zabe da hukumar ta shirya, wanda kuma hakan ne ya sanya aka kammala zaben cikin nasara.

Daraktan watsa labarai na hukumar ne Segun Adeogun ya bayyana wa manema labarai haka jim kadan da bayyana sakamakon zaben. Ya ce “zaben da muka yi a Kogi ya yi kyau, zaben da muka yi a Adamawa shi ma haka, amma na Sakkwato duk ya fi kyau. Saboda haka kullum muna kara koyon wannan mulki ne na dimokradiyya. A cewarsa.

Hukumar zaben ta bayyana cewa an kada kuri’u 785,682, yayin da kuri’u 698,362, suka zama sahihan kuri’u. Sannan kuma kuri’u 87,320 suka baci. Inda ta bayyana Alhaji Alu Magatakarda da cewa ya sami kuri’u 562,395, inda ya doke Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi, wanda ya sami kuri’u123,046. Alhaji Aminu A. Salah Tauma na jam’iyyar CPP ya zo na uku da kuri’u 6,286. Shi ma kuwa dan takarar jam’iyyar ANPP, wanda Gwamnatin PDP ta ba shi Ambasadan Nijeriya a kasar Iran, Alhaji Abubakar Chika Sarkin Yaki ya zo na hudu ne da kuri’u 1,842. Sannan dan takarar jam’iyyar PPA Alhaji Bello Ibrahim Gusau, ya zo na biyar da kuri’u 1,658.





Komawa Shafin Farko