www.dillaliya.freeservers.com

Manchester United da Portmouth:
Za su yi wasa a Abuja

Daga Abdullahi Tumburkai

Your citydon bai wa masu sha’awar kallon kwallon kafa damar kallon wasu daga cikin kwararrun ’yan wasan da ke wasa a kasar ta Ingila.

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Portmouth (Pompey) Harry Redknapp, wanda har yanzu ke cike da farin cikin nasarar cin kofin FA da kungiyarsa ta yi bisa kungiyar kwallon kafa ta Cardiff a filin wasa na Wembley a ranar Asabar din makon jiya ne ya bayyana cewa jaruman ’yan wasan nasa za su zo kasar da ta fi kowacce kasa tasiri ne a Afirka a zagayen da kungiyoyin wasan kwallo ke yi don motsa jini kafin a shiga sabuwar kakar wasan ne a watan Agusta mai zuwa.

Ya kara da cewa wannan ziyarar da za su kawo Nijeriya za ta hada da yin wani kasaitaccen wasa tsakanin Portmouth da Manchester United a babban birnin tarayyar Nijeriya Abuja.

Wasan dai wanda har yanzu a hukunce ba a bayyana ranar da za a gudanar da shi ba, zai zama wasan share fage ne tsakanin kungiyoyin biyu, domin kafin a fara wasannin kakar wasa mai zuwa za su kara a gasar cin kofin Community Shield, wanda bisa al’ada ake bugawa tsakanin wanda ya ci kofin Firimiya da kuma wanda ya ci kofin FA.

Portmouth dai sun yanke shawarar zuwa Afirka ne bayan nasarar da suka samu a irinta da suka kai Hong kong a nahiyar Asiya bara. Kuma hakan na nufin cewa ’yan wasan Portmouth Kanu wanda ya ci kwallon da ta kai ga lashe kofin FA a makon jiya, da kuma John Utaka wanda shi ne ya baiwa Kanu kwallon da ya ci, dukkansu za su zo kasarsu ta haihuwa ne.

Sai dai kuma shi Harry Redknapp ya bayyana cewa, bai bayya wa ’yan wasansa labarin wannan balaguro da za su yi zuwa Nijeriya ba. “Ban shaida masu ba har yanzu, amma lallai za mu je Nijeriya. Ban sani ba ko za su yi mamakin hakan, amma na san cewa kowa ya ji dadin Hong Kong a bara.”

Za mu yi wasa da Manchester United a can (Nijeriya). Al’ummar can na matukar son ganinmu a can, abin dubi dai kawai shi ne Allah ya sa su ma Manchester suna son can, amma mu kam muna son zuwa can.”

“Idan mun dawo daga Nijeriya za mu sake buga wani wasan da Manchester United a Wembley na cin kofin Community Shield, muna son haka sosai, sai dai a gaskiya ina son zuwa hutu da matata. Ba na tunanin za mu yi wasa a Turai kwanan nan, sai dai akwai wasu wasanni wand kila mu dauki daya daga ciki ko biyu.”

A shekarar bara dai Portmouth sun samu nasarar cin kofin Barclays na Asiya, inda ta ci Liverpool a bugun daga-kai-sai-mai tsaron gida. Gasar da aka shirya ta da makudan kudade, wanda kungiyoyin Fulham, Portmouth, Liverpool da kuma zakarun Hong Kong suka shiga ciki.





Matsa Nan