www.dillaliya.freeservers.com

Me ya sa suke tsoron Goje?

Danjuma GojeMusamman ma idan shi wannan Shugaba yana rike da wani mukami ne na siyasa. Amma wasu daga cikin masu irin wadannan soke-soken ba su damu ba idan ma wanda suke sukan yana yin aikin da ya kamata a mukaminsa. Ta yiwu masu irin wannan hali suna neman suna ne kawai, wanda a kan kansa abu ne mai kyau, wanda kuma ba ni da matsala da shi, amma in an yi shi bisa bata sunan wasu, to sukar ta rasa karsashinta da kyakkyawar manufarta. Amma kuma ai ba kowane mutumin gari ne ke samun ganin sunansa a jarida, balle kuma batun a ambace shi a labaran kasa na talabijin ba.

Wannan ya sa na tuna zancen Ralph Waldo Emerson, wani mashahurin mawakin zube, Ba’amerike kuma marubuci wanda ya ce, “In dai za ka zama babban mutum, to sai an kasa fahimtar ka.” Manyan mutane ne kawai ake magana a kansu, kuma ba kowa ke yi ba sai masu karamin tunani! Kuma ga tambaya ga masu suka din nan wadanda suke bata sunan shugabanni jama’a cewa, suna nufin su ce ne ba wani abin kirki da irin wadannan shugabanni suka yi? Tunda dai sanin kowa ne cewa a doron kasar nan dai mutum tara yake bai cika goma ba. A kan kowa akwai mai kyau da mara kyau, to maimakon magana a kan rashin kyawun, me zai hana a raini abin kirkin da ke tattare da mutum don amfanin jama’a gaba daya?

A ’yan kwanakin nan, Gwamna Muhammad Danjuma Goje yana shan suka a gun jaridar LEADERSHIP. Da farko suka sa shi a cikin jerin sunayen mutane goma da aka fi tsana a Nijeriya, sannan a shafin jaridar na farko na ran 7 ga Mayu, 2008, amfani da ya yi da damar da doka ta ba shi, sai aka bayyana shi da “damfara.” Yayin da a ranar 27 ga Afrilu, 2008 Gwamna Goje ya bayyana kudin fenshonsa, abin da yake yi a lokacin yana kan doka. Bisa shawarar Hukumar tattara rabenu ta kasa (RMAFC) da ke Abuja, Majalisar dokokin jihar Gombe ta amince da kudurin dokar fensho ta jiha. Wannan ya dace da shawarar da Hukumar RMAFC ta ba dukkan jihohi, wanda kuma yake bisa ikon da aka ba Hukumar a karkashin sashi ne 124 (5) na tsarin mulkin 1999 na Tarayyar Nijeriya. A kan haka ne Majalisar dokokin jihar ta Gombe ta yi gyara ga dokokin fensho na masu rike da mukaman zartarwa na jihar na shekarar 2007 da 2008. Wannan doka ta 2008 da aka yi wa gyara ta tanadi cewa dukkan Gwamnonin da suke yin wa’adi na biyu da Mataimakansu za su ci gajiyar tsarin fensho, haka nan kuma wadanda suka yi wa jihar aiki a wadannan matakai kamar yadda sashi na 5 karamin shashi na 3 ya tanada. A hakikanin gaskiya ban san dalilin da wannan mataki da aka dauka bisa doka zai jawo babatu ba. Yaya mutum zai yi aiki sannan a ce ba za a biya shi a wannan duniyar ba? Sannan kuma a yayin da Gwamna Goje ya bayyana nasa cek din a gaban jama’a, ai rahotannin da ba sa karya sun nuna cewa wasu sun karbi nasu ne a asirce. Yanzu ka ce wannan shi ne irin aikin wanda ke so ya boye gaskiya? Gwamna Goje ba shi da wani abin boyewa ko yake jin tsoron bayyanar sa, shi ya sa komai nasa a bayyane yake. Ya kamata ne masu sukar sa su yabe shi saboda wannan abin kirki da ya yi.

Ga wadannan masu sukar da suke tsammanin ba wani abin kirkin da ke aukuwa a jihar Gombe, yaushe ne ranar karshe da suka ziyarci wannan tauraruwar jihar da ke yankin kasa ta jigawa? Ina kyautata zaton cewa ba su da labarin gina hanyoyi 46, wadanda suke tagwaye kuma sun sha kwalta a cikin birnin Gombe kadai da aka yi. Haka nan kuma ba su da labarin tituna 50 da suka kewaye garin na Gombe da aka gina da kuma wadanda suke cikin tsawo da fadin Kananan Hukumomi 11 na jihar ta Gombe. Kafin Goje ya hau mulki a 2003, babban birnin jihar, Gombe, tana alfahari ne kawai da wani babban titi kwara daya da ya keta birnin. Banda wadannan kuma ga wasu ayyukan jin dadin jama’a da aka yi da suka hada da gyaran babban asibitin koyarwa na jihar Gombe da sauran asibitoci da ke cikin jihar. Ga kuma samar da kayayyakin karatu a makarantun firamare da sakandaren jihar, ga shirin samar da ruwan sha na jihar Gombe, da shirin samar da wutar lantarki na karkarar jihar gombe da kuma Jami’ar jihar Gombe da ma filin jirgin sama na kasa da kasa a Gombe; wadannan duk kadan ne daga cikin wasu ayyukan ban mamaki da gwamnatin Goje ta aiwatar. Hujjoji da kuma alamu na irin gagarumin canjin da jihar Gombe ta samu tun lokacin da Goje ya hau kan gadon mulki a 2003 a bayyane suke ga duk wanda zuciyarsa take a bude.

Masu wadannan soke-soken suna ikirarin cewa Gwamna Goje yana daure wa siyasar banga gindi. Wannan ya ba ni dariya matuka ganin cewa zabubbukan da aka yi na Kananan Hukumomi a jihar ta Gombe, an yi su cikin kwanciyar hankali ba tare da wata hatsaniya ko wani tashin hankali ba balle mutuwa. Shin ma wai yaushe ne za a ce siyasar zabe a Nijeriya ba tattare take da siyasar banga ba? To yaya aka yi ba su aiwatar da ta’addancinsu ba a jihar Gombe a zabubbukan Kananan Hukumomi da aka yi. A wasu jihohin ma ai irin wadannan zabubbukan kasa yin su aka yi, a wasu jihohin kuma mummunan tashin hankali ne a ko’ina aka yi zabubbukan, amma kuma babu irin wannan rahoton sam-sam a zaben da aka yi na jihar Gombe. Don haka muna iya cewa kenan Gombe a yau ita ce jihar da aka fi samun zaman lafiya a kasar nan, kuma dukkan wadanda suke ta yin munanan maganganu a kan Gwamna Danjuma Goje ba komai bane face ’yan son a-fasa-kowa-ya-rasa.

Daga abin da na fada, a sarari yake cewa jaridar LEADERSHIP ba wani bincike sahihi da ta yi, kuma abin da ta yi ya saba wa ka’idar aiki. Duk wani dan jaridar da ya amsa sunansa ya kamata ya san cewa bincike a yayin aikin jarida shi ne abin da ya dace, kuma yake jawo daukaka ba kawai a fagen aikin jarida ba, har ma a gun wadanda suke amfani da abin da ’yan jaridan ke sana’antawa. Don haka mawallafin jaridar LEARDERSHIP ya kamata ya rika shirya wa ma’aikatansa taron kara wa juna sani (in bai yin hakan) ko kuma ya rika tura su yin kwasa-kwasan da sanannun cibiyoyi ke shiryawa don ya zamana cewa dukkanin rubuce-rubucensu ba komai bane face gaskiya tsagwaronta wanda shi za a buga jama’a su karanta. Duk kuma da irin yarfen da jaridar LEADERSHIP ta yi a kan Gwamna Goje, jama’ar jihar Gombe ba za su taba daina kaunar Gwamnansu ba, kuma jaridar LEADERSHIP za ta kyautata wa kanta ne idan ta ba da hakuri ga Gombawa ta dai jaridar tasu da suka yi amfani da ita suka bata sunan Gwamnansu, Gwamna Muhammad Danjuma Goje.

Sa hannu

Honorabul Muhammad Bello Sulaiman, dan majalisar wakilai ta tarayya da ke wakiltar mazabar Akko ta Tarayya, jihar Gombe.





Matsa Nan