www.dillaliya.freeservers.com

BUDADDIYAR WASIKA GA MAWALLAFIN JARIDAR LEADERSHIP

A lokacin da kake zaunannen marubuci a jaridar DAILY TRUST, kafin ka ga cewa lokaci ya yi da za ka kafa naka gidan jaridar, a koyaushe kana kan kwarewarka ne, kuma ba ka kyale kowa ba a yayin da kake nuna kishin kasarka wajen ganin an share cutar da ke tattare da mu don ganin kasarmu ta haihuwa ta zama al’umma ta gari mai cike da adalci. A yanzu kuma da kake babban Jami’in gudanarwar gidan jaridarka, hakika kai abin alfahari ne ga aikin jarida a wannan zamani namu.

A zahirin gaskiya dan uwa Sam kasantuwarka a kusan duk wuraren da ke da hadari, shaida ne na irin gwarzon dan jaridar da kake. Alal hakika kana da karfin hali da rashin tsoro, a kan komai, kai mutum ne da ya sadaukar da kansa ga dukkan burin matakin gwamnati na hudu. Za ka yi mamakin me ya jawo duk wannan yabo a kanka, tare kuma da yin budaddiyar wasika, kuma a lokaci guda da zabin wannan jaridar don yin wannan “azarbabin.”

Na tabbata cewa jaridar DAILY TRUST har yanzu gida ce gare ka, saboda duk lokacin da ka ga cewa ya kamata ka rufe shago, to dole “angulu ta dawo gidanta na tsamiya.” Duk da haka dai ina fatan kamfaninka na Leadership Group of Newspapers zai wanzu har illa masha Allahu.

Gudun kar a zarge ni da wuce gona da iri, ina so in jawo hankalinka a kan rahotannin jaridarka na bata suna, musamman na kwana-kwanan nan, sharhin Edita da kuma wasu rubuce-rubucen da suka bayyana a jaridar Sunday Leadership ta 11 ga Mayu, 2008 mai kanu: “Har yanzu a kan Goje da ganimarsa ta Naira miliyan 200.” Cikin raha na kira abin rahoton bata suna, ganin yadda a irin naka salon na cin zarafi wanda bai dace da gogaggen dan jarida irin ka ba, ka gwammace ka zubo kasa warwas a kokarinka na bata sunan Gwamnan jihar Gombe, Alh. Muhammad Danjuma Goje, abin da dama suka gaza a kai.

Saboda yadda cikin arha ka cusa kanka cikin wannan kamfen din bata suna, wannan ya nuna a sarari kai ba dan jaridar da ake mutuntawa bane a wannan zamani da da damanmu muka dauke ka, amma wanda a yanzu abin kunya ya tube rigarsa ta ’yan jarida ya musanya ta da wani abu mai arha, wanda ya cancanci dan dagajin dan siyasa ne kawai. Duk da cewa ni ina goyon bayan aikin jarida na hakika, to bisa la’akari da ka’idojinsa ba wani laifi da aka yi idan ka zurfafa bisa ka’idojin rashin nuna son kai a cikin bincike-bincikenka, wanda ya dace da ka’idojin aikin jaridar. Shi aikin jarida ai ya doru ne a kan rashin nuna ta’assubanci kowane iri ko nuna kiyayya da wani mutum ko wani mai rike da mukamin gwamnati, sabanin abin da rahotannin jaridarka da kuma ra’ayin Edita na jaridar ranar 11 ga Mayu, 2008 suka nuna. A gaskiya ina kin aikin jaridar da ake yin sa don tsorata jama’a, abin da wasunku wani lokaci suke yi don dai a san da su, a yayin da suka ga komai ya gaza musu.

Ka lura da zancena dan uwa Sam, ba ina magana ne a madadin Gwamna Goje ba ko kuma a irin kalmominka “al’amarin ba shi da kariya,” a filinku na ra’ayin Edita na Sunday Leadership din 11 ga Mayu, 2008. Alal hakika a matsayina na mai kishin kasa ina da dukkan damar in kare Gwamnanmu yadda ya kamata kuma ta kyakkyawar hanya, amma ba ta irin babatunka ba, wanda ga duk wani mai hankali ya san yana warin banzatar da aikin jarida kuma cike da shakku. Bisa ka’idojin dimokradiyya ban ga ta inda Gwamnanmu ya aikata wani abin da ya saba wa tsarin mulki ba. Mutum ma ya ce Gwamna Goje ko tantama babu Gwamna ne na jama’a kuma zai ci gaba da kasancewa haka, wani abu ne da ba a musun sa. Zarge-zargenka kan kuskure suke matuka, kuma sun yi hannun riga da gaskiyar al’amuran da ke kasa. Kuma ganin ka kasa gamsar da ni da ire-irena, a sarari ya nuna irin rawar wa kake takawa. Duk da cewa ina girmama ka saboda salonka na bincike a aikin jarida, wanda ya dace da aikin naka, amma a wannan karon ba ka burge ni ba da salonka na ’yan dagajin aikin jarida, wanda kyawunsa a tsince shi a bola.

Dan uwa Sam, muna cikin wani lokaci ne na yarfen siyasa da kulla makirci, to don kawai ka bata wa mutum suna sai ka shafa masa kashin kaji ba wani sabon abu bane a wannan marra. Ni kaina da kuma Gombawa da yawa masu son ganin ci gaba ba za su yi mamaki ba don ka shirya ka bata sunan Gwamnanmu don taka manufar. Ga fa abin da ka ce: “babban kuka a kan gagarumar satar Goje,” a gaba kuma ka ce, “wannan wata alama ce ta sauyawar tunani.” Ban gushe ba ina ta mamakin wannan “satar” da kake magana a kai. Da kuma dangane da “sauyin tunanin” da ka ce. Lalle kam mun yi tunani kafin mu zabe shi a karon farko da kuma karo na biyu a matsayin Gwamnanmu. Don haka wannan kukan na menene dan uwa Sam?

Kuma mu waiwaya baya tun daga lokacin da aka kirkiro jihar Gombe a ranar 1 ga Oktoba 1996. Ta yi Kantomomin mulkin soja biyu da Gwamnan farin hula daya, zamanin shekaru bakwai a tsakaninsu, in ka kwatanta Gombe babban birnin jihar a yadda take yanzu cikin shekaru hudu, ko kai da yanzu ka mai da kanka dan adawar Gwamna Goje, za ka yarda cewa an ci nasarori da dama. Duk yadda ka yi, ba za ka iya hana wa Gwamna Goje matsayin da ya kamace shi ba in ana lissafa wadanda suka yi wa kasar nan aiki tukuru.

Shawarata a nan gare ka dan uwa Sam shi ne kar ka yarda kai din da muka sani wasu bata garin ’yan siyasa wadanda haskensu ya gushe, wadanda a zamaninsu sun samu damar da za su yi wa jama’a aiki, amma ba su yi ba, suka bari kyashi da hadama suka rufe zukatansu su yi amfani da kai, su yi girbi a inda ba su yi shuka ba. In dai ba kana da naka zafin da kake ji a kan Gwmananmu ba, to ba kai ka cancanci ka yi magana a madadin EFCC ko Majalisar dokokin jihar Gombe ba, wadanda suke da kaifin ido da kwarewa da iko da sararin gano wanda ke cin hanci ko ba ya ci ba, ba kawai ga jaridarka ba wacce a bincikenta na son kai da rashin kan gado, ko kunya babu ta ce wai Gwamna Goje shi ne na biyu a cikin mutanen da suka fi kowa cin hanci a kasar nan a yau. Wannan wane irin rashin kan gado ne! Kuma a gaskiya zan iya cewa kana fama da rashin sanin kan gadon tarihi. Ni kaina da kuma dukkan Gombawa da ma dukkan ’yan Nijeriya suna masu tir da wannan zayyanawar taka gaba dayanta. Domin in tabbatar da ikirarina dan uwa Sam, ka manta cewa kai da jaridarka a baya can kun ce tsohon Gwamna Saminu Turaki shi ne Gwamnan da ya fi kowa wanda jihar Jigawa da jama’arta suka taba samu? Yanzu kuma da ka sauya rawa daga tsananin kaunar da kake wa Saminu Turaki bayan Hukumar EFCC ta same shi da laifi na almundahanar biliyoyin Naira na kudin jihar, ya nuna irin munafuncin da ke tattare da kai. Me ya samu Gwarzonka a yanzu dan uwa Sam? Wa ke yaudarar wani?

Tashin farko, Gwamna Goje ya yi alkawarin zai sadaukar da kansa ga mutanen jihar Gombe awwalan kafin wani abu bayan an rantsar da shi Gwamna a ran 29 ga Mayu 2003. Ya fadi a sarari cewa ba zai bari wasu ’yan tsiraru da kwadayinsu shi ne zuke kudin jama’a ba ta hanyar samun kwangiloli masu tsoka, wanda ba aiwatarwa za su yi ba illa su cinye kudin. Wannan da ma wasu dalilan, suka bata musu rai, shi ya sa suka koma ga yin amfani da bata suna da kage da kuma shawo kan ire-irenka su amince da maganganunsu cewa Gwamna Goje ba mutumin kirki bane, wanda kuma mafarkin kawukansu ne kawai.

Zargin Gwamna Goje kai tsaye yana da nasa fassarar a shar’ance. Ga yawancinmu ba ma kallon abin da ka yi a matsayin “ba makawa,” saboda in aka yi la’akari da irin amsar da ka bayar da kuma kokarin biyan bukatar kanka da na wadanda suka dauke ka aiki a wannan mugun wasa. Abin da ka yi ya zubar da mutuncin kanka ne a idon masu kaunarka, ciki har da ni kaina. Ka san cewa za a iya kai karar ka kan bata suna in aka yi la’akari da irin hujjojin da kake da su a rubuce-rubucenka.

Ba ka da wata madafa idan Gwamna Goje ya zabi ya kai karar ka da jaridarka kan bata masa suna a matsayinsa na wani babban Jami’in Gwamnati, saboda ba ka da wasu kwararan shaidu. In ba ka sani ba, ’yan majalisar dokokin jihar Gombe ba irin kidahuman nan bane, saboda yawancinsu kwararrun ma’aikata ne a fagagensu na ayyukan dan Adam, kuma suna da sani fiye da yadda kai kake zato. Don haka ka koma kana zargin Gwamna Goje da “murda kambin ’yan majalisar dokokin jihar Gombe,” alhali akwai kyakkyawan dangantaka tsakanin matakan gwamnatin guda biyu, yana wofintar da irin bincikenka. Majalisar dokokin jihar Gombe, ita ma tana da hakkin ta kai karar ka saboda kokarin da ka yin a ka nuna ta a wani irin kama da ke bata matsayin ta na wani muhimmin bangare na gwamnati duk da dimbin masu alfarmar da ke cikinta.

Matsalar ’yan Kalare kuwa, ai Gwamnatin Goje ta gaje ta ne daga gwamnatin da ta gabace ta. Irin wannan shi ne matsalar Udawa, wadanda suke bice kauyuka, suna kisa, fyade da jikkata mutanen da ba su ji ba su gani ba a kauyuka, ba a ta batun ’yan fashi wadanda suke munanan ayyukansu da rana tsaka. To, yanzu duk wadannan matsaloli sun zama tarihi saboda Gwamna Goje bai yi kasa a gwiwa ba sai da ya tabbatar da cikakkiyar zaman lafiya da tsaron rayuka da na dukiyoyi a jihar Gombe. Za ka yarda da ni cewa dukkan masu rike da mukaman gwamnati na siyasa tun daga kamawar wannan jamhuriya ta hudu sun mai da siyasar banga a matsayin abar dogara a dukkan wuraren kamfe dinsu. Don haka a yayin da Gwamna Goje ya shiga ofis, farkon abin da ya fara yi shi ne fuskantar wadannan matsaloli don shawo kansu, a inda ya kashe makudan kudade don ya mai da jihar amintatta ga kowa. Yanzu haka Gome, babban birnin jihar ta fi aminci fiye da yawancin biranen kasar nan a yau. Sam-sam Gombe ba tana cikin “kawanya” bane, kuma Gwamna bai taba alfaharin cewa shi Shugaban ’yan banga bane kuma yana fitar da su ga wasu jihohi makwabta.” Wannan karya ce tsagwaronta, kuma kai ka sani sarai cewa dukkanin jihohin nan 36 suna da nasu irin matsalolin da suke fama da su ba tare da sun jira wani ya “shigo” musu da matsalarsa ba. Abin farin ciki shi ne mutanen da suke fakewa da sunan Gwamna Goje don su bata sunansa an gano su kuma tuni aka fitar da su, sun kuma san kansu.

Gaskiya ne cewa saukin halin da Goje yake da shi a siyasance ya zama wani abin damuwa ga wadanda suka mai da kansu dattawan siyasar Gombe, alhali a hakikanin gaskiya ba su yi wani abu da za su cancanci wannan babban matsayi abin girmamawa ba, don haka suka gwammace su yi amfani da salon kautar da hankulan jama’a daga al’amuran ci gaba da kiran Gwamna da wasu sunaye tare da zargin sa kan laifuffukan da bai san da su ba, suna amfani da ire-irenku ku zartar musu da mummunan aikinsu. Su ma a koyaushe suna kai wa juna iya wuya ne ta hanyar nuna wa juna kyashi da sauransu. Duk kuma da irin wannan mummunan hali na kwance wa juna zani a kasuwa, yaushe suka daina kawo wa gidan Gwamna Goje ziyarar dare suna neman taimakon kudi?

Duk da yadda za ka nuna kai makaho ne ga ci gaban da muka samu a babban birnin jihar da kewayenta, ba kuma zan yi mamaki ba idan a lokaci guda ka kasance kurma ga muryoyin hankali da za su yi magana da kai. Ba tare da wani cika baki ba, jihar Gombe ita ce jiha ta biyu ta fuskacin ci gaba a bayan jihar Barno a yankin Arewa maso gabas. Har ila yau kuma babban birnin jihar shi ne cibiya kuma matattarar kasuwanci a duk fadin yankin Arewa maso gabashin kasar nan. Me ya sa haka? Kudurin da Gwamna Goje yake da shi na samar da abubuwan more rayuwa hakika ya biya, kuma manufarsa ta barin kofa a bude ga dukkan ’yan Nijeriyan da suke so su zo su zuba jari a Gombe ya sa ta zama daya daga cikin biranen da suka fi saurin bunkasa kuma mafi zaman lafiya a biranen Nijeriya. Shi ya sa ma ba abin mamaki bane da ya zamana cewa Gwamnatin Tarayya ta ga cewa zai fi dacewa ta aje ofishin Hukumar albarkatun man fetur (DPR) a Gombe, haka ma babban bankin Nijeriya (CBN) da wasu Hukumomin gwamnatin Tarayya, har da ma kungiyoyin kasa da kasa.

Gwamna Goje cikin natsuwa yake da jin dadi ba tare da ya biya ko ya dauki wasu su rika “kore masa wari” ba. Dan kasa na gari yana Magana, amma ba da baki ba, ta hanyar aikinsa, wanda ana iya ganin sa a sarari a irin ayyukan da ya yi ya zuwa yanzu ga mutanen jihar Gombe. Shi ba kamar sauran takwarorinsa bane wadanda suke jin dadin ganin ’yan jarida suna kuranta su, su kuma suna shagwaba su da ba su na goro daga kudin jama’a. Tabbas Gwamna Goje ba zai yi irin wannan abu ba. Gwamnonin da ake ma kuranta su din a kan karya, yanzu ko kunya babu, EFCC tana tuhumar su inda suke fuskantar tuhume-tuhumen da suka shafi almundahanar kudade. Ko da Obasanjo ko ba shi, Gwamna Goje zai iya tabbatar da kansa da kuma yin bayanin irin ayyukan bauta wa kasa da ya yi wa jihar Gombe da mutanenta.

Hakika ka sani cewa Janar Muhammadu Buhari ya yi imani da tsare gaskiya da aiki tukuru. Wane irin sharhi ya yi kan Gwamna Goje, ba jimawa da aka rantsar da Goje a matsayin Gwamnan Gombe sa’ilin wata ziyara da ya kai jihar ta Gombe? Bai zargi Gwamnonin da suka yi mulki a jihar ba saboda kasa tsinana wani abin a zo a gani ga jihar tun sad da aka kirkire ta? A sarari ya fito ya yaba wa Gwamna Goje saboda ayyukan da ya yi da yawa cikin lokacin kankani da hawansa mulki in aka kwatanta da Gwamnonin wasu jihohi. Ka tuna dan uwa Sam cewa Buhari da Abubakar Hashidu ’yan jam’iyya daya ne a wancan lokacin, ANPP, amma Janar din bai tsame abokan siyasarsa daga bulaliyarsa ba saboda sun kasa yin komai ga jihar. A matsayinsa na mutumin kwarai Janar Buhari bai taba boye kiyayyarsa ba ga ’yan kasa marasa kishi ba. To waye dan uwa Sam da har zai kalubalanci kyakkyawan sharhin da Ubangidansa ya yi a kan wani? Ban ga wani dalili da kake da shi ba da za ka koma wa amfani da kamfen din bata suna ba kan mutum mai sadaukarwa kamar Gwamna Goje, alhali Oganka (Janar Buhari) yana da hujjojin da suka sa ya yi yabo a kan Gwamna Goje na madalla da ayyukansa. Ka ga inda ka kuskure ko dan uwa?

Duk da abubuwan da aka farfada, ni ina ganin wani dalilin da ya sa ka tasa Gwamnanmu a gaba ba zai rasa nasaba da yadda ya ki ya ba ka cakin Naira miliyan biyar ba a matsayin nasa gudummawar don aiwatar da taron kwana biyu kan “rashin masana’antu a Arewa” da kamfanin jaridarka ya shirya a Abuja tsakanin 4 da 5 ga watan Maris 2008 ba. Don Allah Gwamnoni nawa ne suka halarci taron? Ko ko kiyawar da Gwamna Goje ya yi na ya turo kudin da aka nema ya isa ya zama gamsasshen dalilin da zai sa a rika sukar shaksiyyarsa da dukkan munanan kalmomi? Irin aikin jaridar nan na tsoratarwa daga naka bangaren ba a da bukatarsa. Ka tuna duk wanda ke zaune a cikin gidan gilashi, to kar ya kuskura a yi wasan jifa da shi. Ina maka kallon gogaggen dan jarida wanda ba zai zubar da mutuncinsa ba ya yiwo kasa a madadin aikinsa, ta yadda zai rika yi wa wasu mummunan aiki ba, saboda in dai kana so ka shigo wanan fage ne a matsayin dan siyasa na gidi, to ana maraba da kai, amma ba ka tsaya kana fakewa da aikin jarida ba. Gwamna Goje ba zai ba da kai ga irinku ba, ya riga ya yi kumbar da ba ya tsoron susar irinku, kuma zai ci gaba da yin abin da zai amfani mutanensa. Lalle ka kauce wa wannan bakar siyasa ta bata suna da bakar gaba. Idan Allah Madaukaki ya kaddarta cewa Gwamna Goje sai ya wuce Gwamna a gaba, to ba wani wanda ya isa ya hana haka aukuwa, ko da kuwa kai ne dan uwa Sam. Ba wanda za a ce yana da laifi sai an tabbatar da laifinsa. Yau da za a ce za a cire sashen tsarin mulkinmu da ya bai wa Gwamnoni masu mulki kariya, to da duk da haka Gwamna Goje zai rika aikinsa ne cikin ’yanci a ko’ina a kuma koyaushe.

Karajin da kake yi a kan Naira miliyan maitan ba a da bukatarsa, ko kana nufin ka ce tsarin mulkinmu fankan fayo ne? Abin da aka yi a bisa ka’idar tsarin mulki, tsare gaskiya da bin ka’ida a kan idon jama’a ya dace da shari’a, ko ko kana musan haka ne?

Dan uwa Sam kada ka yarda hadama ta bata kyakkyawan sunan da kake da shi. Ka dauki Gombe a matsayin gida, mu kuma duk ’yan uwanka, ciki har da Gwamna kansa. Ni na yi imani cewa ba ya kule da kai, kuma haka zai ci gaba. Menene naka na ta da kura kana shirin fada alhali dukkan zarge-zargenka ba su da tushe balle makama?

Ga Gwamnanmu mai sadaukar da kai kuwa, shawararmu a nan ita ce ka kau da kai daga wadannan masu sukar ba gaira ba dalili, wadanda ba za su taba ganin abin kirki ba a abubuwan da kake yi, ba wani abin da zai dame ka. Mu Gombawa muka fi dacewa mu gaya wa duk wani mai shakku irin nasarorin da ka samu.

Muna karfafa maka gwiwar ka ci gaba da ayyukan kwarai da ka soma, ka ba makiyanka kunya. Muna tabbatar maka da dukkan goyon bayanmu. Ba ma mu kawai Gomabawa ba, dukkan ’yan Nijeriya suna alfahari da gagarumar nasarar da ka samu. Jihar Gombe ga ’yan Nijeriya da dama, ba kawai tauraruwar yankin jigawa bace, amma wata aljannar masu zuba jari ce, kuma wata kasar baiwa, zaman lafiya da ci gaba, ta dalilin Gwamnan mutane, Gwamna Goje, wanda ya yi ayyukan da ake kyashi na daukaka jin dadin jama’a.

A karshe dan uwa Sam ya kamata ya sani cewa gabaki dayan ’yan majalisar dokoki na jihar Gombe suna bayan Gwamnansu. Ya riga ya kafa duga-dugansa a kasa, kuma tasirin manyan nasarorin da ya samu za a ci gaba da ganinsu ga ’ya’ya da jikoki masu zuwa.

Dan uwa Sam, a matsayina na wanda ke ganin mutuncinka kasantuwar ka dan jaridan da ya yi suna kuma mai kwarjini, wanda mu ’yan wannan zamani muke alfahari da kasantuwarka cikinmu, ina kira da kakkausar murya a gare ka da ka dawo daga rakiyar abin da aka dora ka a kai na kin Gwamnanmu. Kai abin alfaharin zamaninmu ne, kuma abin bakin ciki ne idan ka kyale aka ja ka cikin murda-murdar siyasa. A yayin da nake maka fatan alheri a duk abubuwan da ka sa gaba, addu’ata ita ce jaridarka ta ci gaba da karfafa. Sunan ‘Leadership’ zai ci gaba da ba da shugabanci, a yayin da wasu ke bi. Allah ya yi maka albarka.
Allah ya ja zamanin Gwamna Muhammad Danjuma Goje!
Allah ya ja zamanin jihar Gombe!!
Allah ya ja zamanin Tarayyar Nijeriya!!!
Sa hannu:
Honorabul Inuwa Garba (Zannan Yalmatu)
Mataimakin Kakakin Majalisar dokoki ta jihar Gombe.





Komawa Shafin Farko